N620 Duk Lita: 'Ba Abinda Muka Zaɓa Ba Kenan', Masoyin Tinubu Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa

N620 Duk Lita: 'Ba Abinda Muka Zaɓa Ba Kenan', Masoyin Tinubu Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa

  • Wani masoyin Tinubu mai suna Adamu Salihu, ya koka kan tsadar rayuwa da ake ciki sakamakon cire tallafin man fetur
  • Ya bayyana cewa halin da ya tsinci kansa a ciki ka iya janyo masa faɗawa hanyar da ba ta dace ba
  • Ya kuma ƙara da cewa yaransa yanzu haka duk sun koma tallar awara saboda ba zai iya ci gaba da biya musu kuɗin makaranta ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Wani mazaunin Kano mai suna Adamu Salihu, wanda kuma masoyin Shugaba Tinubu ne, ya koka kan tsadar man fetur da ta janyowa 'yan Najeriya shiga cikin mawuyacin hali.

Tun bayan cire tallafin man fetur da shugaban ya yi a farkon mulkinsa, an samu hauhawar farashin man daga naira 195 zuwa naira 530 a duk lita.

Sai dai kuma a wayewar garin ranar Talata, an samu cewa man ya yi tashin gwauron zabi zuwa naira 617 a Abuja, da kuma 620 a Kanon Dabo.

Kara karanta wannan

Saura Kiris Shugaba Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Kudirin N200k a Matsayin Mafi Karancin Albashin Ma'aikatan Najeriya

Masoyin Tinubu ya koka kan tsadar rayuwa
Masoyin Tinubu ya koka kan yadda tsadar man fetur ta tilastawa yaransa daina zuwa makaranta. Hoto: Daily Trust, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu (Facebook)
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masoyin Tinubu ya ce tsadar za ta iya sanya shi aikata wani abinda bai kamata ba

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, Adamu Salihu, wanda ya ce shi ɗan asalin ƙaramar hukumar Bichi ne, ya ce akwai yiwuwar halin matsi ya sanya shi bin hanyar da ba ta dace ba.

Ya ce sabon farashin man da aka samu ya jefa rayuwarsa da ta iyalansa cikin mawuyacin hali.

Ya ƙara da cewa ba abinda suka zaɓa ba kenan shi da 'ya'yansa, inda ya ce abinda suke gani a yanzu ba shi suka yi tsammani ba.

Adamu ya ce yaransa sun bar makaranta sun koma tallar awara

Adamu ya koka kan yadda yaransa suka daina zuwa makaranta saboda ba shi da halin ci gaba da ɗaukar nauyinsu.

Ya ce idan ba a samu sauyi a nan kusa ba, zai cewa yaran nasa su daina yin zaɓe, saboda yanzu haka yaran sun koma tallar awara, ba sa zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Shugaban APC Ya Hakura da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Kujerarsa

Adamu wanda ya bayyana cewa ya daɗe yana siyasa tun lokacin NRC da SDP, inda ya ce rashin wakilai na gari ne ya sa aka shiga halin da ake ciki a yanzu.

An bayyana cewa dogon layin gidan mai da aka rabu da gani tun kwanakin baya ya dawo a mafi yawa daga gidajen man da ke Abuja da Kano.

Kungiyar kwadago ta ɗau zafi kan ƙarin farashin man fetur

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa kungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), ta ce 'yan Najeriya ba za su amince da sabon farashin man fetur da aka ƙara ba.

Kungiyar ta ce ƙarin farashin man zai kasance babbar barazana ne ga fannoni da dama na rayuwar 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel