Rade-Radin Minista: Jigon NNPP a Kano Ya Karyata Labarin Samun Mukami a Tarayya
- Abdulmumin Jibrin ya shaidawa Duniya cewa ba a fitar da sunayen wadanda za su zama Ministoci ba
- ‘Dan majalisar wakilan tarayyan ya nuna maganar ba shi wannan kujera, ba komai ba ne illa karya
- Idan Jibrin ya yi nasarar zama Minista, zai wajaba a gare shi ya ajiye kujerar wakiltar Kiru da Bebeji
Abuja - Abdulmumin Jibrin ya fito karara ya musanya maganar cewa an ba shi kujerar Ministan tarayya a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
A wani matukar takaitaccen bayani da ya yi a shafin Facebook, Hon. Abdulmumin Jibrin ya nuna jita-jitar da ake yadawa sam ba gaskiya ba ce.
Jibril mai wakiltar Kiru/Bebeji a majalisar wakilan tarayya ya nuna labarin karya ne yake yawo, ko da dai bai yi wani bayanin abin da yake nufi ba.
“Jerin bogi. Labaran bogi’
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Abdulmumin Jibrin
Martanin mutane a Facebook
Legit.ng Hausa ta fahimci mutane fiye da 1000 sun maida masa amsa, da-dama su na fatan Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya zama Ministan kasar.
Wani Abdulrasheed Abdulrahman ya rubuta:
"Haka zalika a jerin asali da za a fitar, Ganduje zai samu shiga idan Allah ya so."
“To, ran ka ya dade, a nuna mana jerin ainihi.” Inji Amos Lukman
Wani Bawan Allah daga Bauchi, Faisal Dabo Othman ya ce:
"Mu na yi wa Ganduje fatan alher. Allah ya yi masa Minista. Ni ‘Dan Bauchi ne Wallahi Tallahi idan za a ba Ganduje Minista, a hana Bauchi gaba daya ina son haka balle ta wajensa."
Tijjani Amsko ya ce:
"Mu dai fatanmu Allah Yasa ya tabbata. Gaskiya mu na bukatarka har gobe"
A shafinsa na Twitter, Shehu Sani ya ce jerin sunayen mutanen da ake yama-didi da su a matsayin sababbin Ministoci zai iya zama labarin bogi ko duba.
A sanadiyyar haka ne Farfesa Pat Utomi ya fitar da jawabi ta bakin Darektan sadarwa da yada labaransa, Charles Odibo ya ce ayi watsi da jita-jitar nan.
Kafin yanzu an kawo rahoto cewa Tinubu ya zabi mutane 27 da zai ba kujera a FEC. Wannan karo a cikin sunayen da aka fitar har da Abdulmumin Jibrin.
Ba a zabi Ministoci ba - Aso Rock
A baya an ji Dele Alake ya na irin wannan bayani, ya ce labarin da ya shahara a wajen mutane kwanaki na fitar da sunayen Ministoci ba gaskiya ba ne.
Mai taimakawa shugaban kasar ya ce Mai girma Bola Ahmed Tinubu ne kadai yake da ikon ya zabi mutanen da yake sha’awar aiki da su a gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng