"Da Gangan Na Kulle Iyakokin Kasar Nan, Daga Baya 'Yan Najeriya Sun Yaba", Shugaba Buhari

"Da Gangan Na Kulle Iyakokin Kasar Nan, Daga Baya 'Yan Najeriya Sun Yaba", Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana sane ya sanya aka garkame iyakokin ƙasa na ƙasar nan
  • Shugaban ƙasar ya ce duk da ya sha suka kan wannna matakin ɗa ya ɗauka, daga baya ƴan Najeriya sun koma jinjina masa
  • Shugaba Buhari ya ce ƙasar nan tana da albarkatu da dama don haka dole ne ƴan Najeriya su riƙa samar da abincin da za su ci da kansu

Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ya kulle iyakokin ƙasa na ƙasar nan ne, domin ya ƙarfafawa ƴan Najeriya guiwa su riƙa samar da abincin da za su ci.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa duk da an soki wannan hukuncin na sa da farko, daga baya ƴan Najeriya sun koma suna yabawa, rahoton The Cable ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: NAHCON Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Ƙarin Ƙuɗin Kujerar Hajjin Bana 2023

Shugaba Buhari ya bayyana dalilin kulle iyakokin kasar nan
Shugaba Buhari wajen kaddamar da sabuwar hedikwatar hukumar Kwastam Hoto: @Buhari Sallau
Asali: Twitter

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata, lokacin da ya ke ƙaddamar da sabuwar hedikwatar hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa, wacce ta laƙume N19.6bn wajen ginata.

Sabuwar hedikwatar tana a yankin Maitama, cikin babban birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Buhari ya yi nuni da cewa Allah ne kaɗai zai iya kare iyakokin ƙasar nan saboda tsawon da su ke da su, cewar rahoton The Nation.

A kalamansa:

"Ina son ku sani cewa daga tafkin Chadi zuwa Benin Republic ya fi tsawon kilomita 1,600, don haka Allah ne kawai zai iya kare iyakokin nan. Ana buƙatar mutumin da ya cancanta da ƙarfin da zai iya sanya ido a kai."
"Da gangan na kulle iyakokin ƙasar nan saboda na san ƴan Najeriya, za su yi odar shinkafa, su kai wata Nijar da sauran ƙasashe, sannan su shigo da shinkafar nan."

Kara karanta wannan

Bikin Rantsar Da Tinubu: Abubuwa 7 Da Buhari Zai Yi a Satin Ƙarshe A Matsayin Shugaban Najeriya

"Da arziƙin da mu ke da shi, mu na da mutane, mu na da ƙasa da yanayi mai kyau. Ƙasashe nawa ne su ke da sa'a a duniya kamar Najeriya, ƙasashe ƴan kaɗan ne.
"Don haka kulle wannan iyakar mai tsawon kilomita 1,600, ƴan Najeriya sun haƙiƙance sai sun ci shinkafa ƴar waje. Ko dai ku ci abinda ku ka noma ko ku mutu. Na yi ƙoƙarin bayyana matsayata, sannan daga baya ƴan Najeriya sun yaba da hakan."

Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

Da zu rahoto ya zo cewa , shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka guda takwas da gwamnatinsa ta aiwatar.

Shugabam ƙasar zai ƙaddamsr da aikin titin Kaduna-Kano, gadar Niger ta biyu da sauran wasu muhimman ayyuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel