Shugaban APC na Kasa Ya Yi Muhimmin Kira Ga Shugabannin Majalisa, Ya Bayyana Hanya 1 Da Za Su Taimaki Tinubu

Shugaban APC na Kasa Ya Yi Muhimmin Kira Ga Shugabannin Majalisa, Ya Bayyana Hanya 1 Da Za Su Taimaki Tinubu

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya buƙaci shugabannin majalisa da su marawa Shugaba Tinubu baya
  • Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa ta hanyar hakan ne shugaban ƙasar zai samu ya sauke nauyin da ke kansa
  • Abdullahi Adamu ya kuma buƙace su da su haɗa kawunansu domin ta hakan ne kawai za su iya kawo ayyukan ci gaba a ƙasa

Keffi, jihar Nasarawa - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya buƙaci shugaban majalisar tarayya da su kawo tsare-tsare waɗanda za su taimaki Shugaba Tinubu ya cika alƙawuran da ya ɗauka.

Premium Times ta kawo rahoto cewa Adamu ya bayar da shawarar ne a ranar Asabar, lokacin da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya jagoranci ƴan majalisar zuwa gidansa da ke a Keffi cikin jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Ziyarci Sarkin Musulmi, Ya Nemi Alfarma 1 Tak

Abdullahi Adamu ya bukaci shugabannin majalisa su yi aiki tare da Tinubu
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu, tare da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Shugaban na jam'iyyar APC ya bayyana cewa haɓya ɗaya da za a taimaki gwamnatin Shugaba Tinubu, ita ce tabbatar da mambobin majalisun guda biyu kawunan su a haɗe su ke.

Ƴan Najeriya na da fata mai yawa akan shugabannin majalisa, Adamu

Sanata Adamu ya ce ƴan Najeriya sun ɗora fata sosai akan shugabannin majalisar kuma za su iya sauke nauyin da ke kansu ne kawai idan sun haɗa kai sun yi aiki tare da ɓangaren zartaswa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A matsayinka na shugaban majalisar dattawa kuma shugaban majalisar tarayya, kana da ilmi, ƙwarewa da sanin yakamatan da zai sanya ɓangarorin biyu na gwamnati su yi aiki tare domin zaman lafiya da ci gaban ƙasar mu."

Adamu ya kuma taya shugaban majalisar dattawan da mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin, kan nasarar da suka samu na zama shugabannin majalisar.

Kara karanta wannan

Faɗa da Cikawa: Gwamnan Arewa Ya Fara Raba Wa Mutane Masu Lalura N6,500 Duk Wata a Jiharsa

Ya kuma ja hankalinsu kan cewa lokacin neman muƙami ya ƙare, yanzu lokaci ne na yin mulki da tabbatar da akwai fahimta mai kyau a tsakanin ɓangaren majalisa da na zartaswa.

An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Nada Magnus Abe a Matsayin Minista

A wani labarin kuma, an buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da ya ajiye tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, daga cikin waɗanda zai ba muƙamin minista daga jihar Rivers.

Wata gamayyar shugabannin jihar Rivers ta nemi Shugaba Tinubu da ya ba Magnus Abe muƙamin minista a cikin ministocinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel