EFCC Ta Karyata Zargin Neman Tsohon Gwamnan APC Ruwa a Jallo

EFCC Ta Karyata Zargin Neman Tsohon Gwamnan APC Ruwa a Jallo

  • Ana zargin cewa Hukumar EFCC ta fara farautar tsohon Gwamna, Bello Muhammad Matawalle
  • Tsohon Gwamnan na Zamfara bai fito ya ce uffan tun bayan da aka fara yada wadannan rahotanni ba
  • Kafin Abdulrasheed Bawa ya bar kan kujerar hukumar EFCC, ya yi ta musayar kalamai da Matawalle

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ayyana Alhaji Bello Matawalle a cikin wadanda ta ke nema.

Rahoto ya fito daga Tribune cewa EFCC ta na farautar Bello Muhammad Matawalle bisa zargin rashin gaskiya da ya tafka a lokacin ya na ofis.

Bello Muhammad Matawalle ya yi gwamna na shekaru hudud aga 2019 zuwa 2023 a Zamfara.

Wani babban jami’in hukumar ya shaidawa Sunday Tribune cewa a ranar Asaba, EFCC ta bukaci DSS ta bada umarnin cafke Bello Matawalle.

Kara karanta wannan

EFCC: Yadda Mutuwar Shugaban Ma’aikatan Buhari, Abba Kyari Ya Yi Waje Da Magu Da Kawo Bawa

Zuwa yanzu ba mu samu cikakken bayanin laifuffukan da ake tuhumar Matawalle da aikatawa ba.

EFCC ta na so jami’an hukumar DSS su bada dama a damke tsohon Gwamnan a duk inda aka gan shi a fadin Najeriya domin ayi bincike a kan shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan shugaban Najeriya ya dakatar da Abdulrasheed Bawa daga kujerar da yake kai na shugaban EFCC.

Kafin a dakatar da Abdulrasheed Bawa, ya fito fili ya na musayar kalamai da tsohon Gwamnan wanda ya bukaci a dakatar da shi daga bakin aiki.

A wancan lokaci Matawalle ya zargi Bawa da neman cin hancin makudan kudi daga hannunsa, ya kuma bukaci EFCC ta binciki Ministocin tarayya.

Rahotan ya ce daga cikin tuhumar da ke kan tsohon Gwamnan shi ne ya karkatar da N70bn daga baitul-mali da sunan kwangiloli a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Zance ya fito: Bayan Ganawar Tinubu Da Dangote Da Matawalle, Batutuwa Sun Fito Waje

Ana zargin cewa jagoran na APC ya na wasan buya da hukumar saboda gudun ayi ram da shi.

EFCC: "Ba mu farautar Matawalle"

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar da jawabi dazu a shafin Twitter, ya na mai musanya wannan rahoto, ya ce babu gaskiya a labarin.

Uwujaren ya ce zuwa yanzu EFCC ba ta ayyana Bello Matawalle a cikin wadanda ake nema ba, kuma ba ta nemi taimakon kowa wajen cafke shi ba.

EFCC ta ce akwai hanyoyin da ta ke bi wajen cafke mutum, ba ta labe da sunan wasu ba.

Wani jami’in EFCC yake fadawa manema labarai cikin gatse ko yaushe rabon da a ga Matawalle a fili. Sai dai babu tabbacin ‘dan siyasar ya boye.

Ko a karshen makon nan, tsohon Gwamnan na jam’iyyar APC ya ziyarci Mai girma shugaban kasa watau Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Ba DSS Sabon Umurni a Kan Godwin Emefiele Da Ke Tsare a Hannunta

Kamar rahoto ya zo, a ranar ne Shugaba Tinubu ya yi kus-kus da Aliko Dangote.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel