INEC Ta Saka Ranar Sake Duba Sakamakon Zaben Da Aka Gudanar A 2023 Don Gyara Matsaloli A Gaba

INEC Ta Saka Ranar Sake Duba Sakamakon Zaben Da Aka Gudanar A 2023 Don Gyara Matsaloli A Gaba

  • Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana ranar sake duba sakamakon zaben da aka gudanar a wannan shekara
  • Hukumar ta bayyana haka ne ta bakin Festus Okoye wanda shi ne shugaban wayar da kan jama'a na hukumar a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni
  • Hukumar ta ce ta fara duba sakamakon zabe tun 2011 don koyan darussa a zaben da kuma hanyoyin inganta shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana ranar da za ta sake duba sakamakon zaben da aka gudanar a watan Faburairu da Maris.

Kwamishina a hukumar kuma shugaban kwamitin kula da wayar da kan jama'a, Festus Okoye ya ce za a fara duba sakamakon ne daga ranar 4 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Agusta 2023.

Kara karanta wannan

Mataimakin Buhari, Farfesa Osinbajo Ya Samu Aikin Farko Bayan Barin Aso Rock

INEC ta bayyana ranar sake duba sakamakon zaben da aka gudanar a 2023
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu. Hoto: INEC.
Asali: Facebook

Okoye ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni.

Okoye ya ce sake duba fasalin zaben zai shafi bangarori da dama

Ya ce sake duba sakamakon zaben zai shafi duk abubuwan da suka faru kafin da lokacin da kuma bayan zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Okoye ya kara da cewa hukumar ta fara gudanar da sake duba sakamakon zaben tun shekarar 2011, kamar yadda Thecable ta tattaro.

Ya ce daga cikin amfanin sake duba sakamakon zaben shi ne koyan darussa a zabukan da kuma neman hanyar kawo gyara a gaba.

A cewar sanarwar:

"Sake duba sakamakon zaben zai fara ne da ganawar kwamishinonin zabe na jiha a ranar 4 ga watan Yuli da karkarewa da bahasin hukumar a ranar 5 ga watan Agusta.
"A matakin jiha, sake duba sakamakon zai kunshi ma'aikatan hukumar da na wucin gadi da malaman zabe da kuma dukkan jami'an zabe.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamna Zai Ba Mazauna Garuruwa Makamai Domin Yakar ‘Yan Bindiga a Arewa

Karin wadanda abin zai shafa yayin gudanar da sake duba zaben

Sanarwar kamar yadda Legit.ng ta tattaro ta kara da cewa:

"Daya bangaren ya kunshi masu ruwa da tsaki da suka hada da jam'iyyun siyasa da jami'an tsaro da masu kula da zabe da kuma 'yan jaridu.
"Sauran sun hada da direbobi da suka yi jigilar kayan aikin zabe zuwa wurare daban-daban."

Lauya Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Korar Shugaban INEC

A wani labarin, wani fitaccen lauya, Malcolm Omirhobo ya bayyana cewa Tinubu ba zai iya korar shugaban Hukumar INEC ba.

Lauyan shi ne wanda ya yi wata irin shiga ta bokaye a watan Yuli na shekarar 2022 a zaman kotun koli.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Lauyoyi ta Kasa, Olisa Agbakoba ya bukaci Shugaba Tinubu ya kori shugaban hukumar INEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel