Shettima da Matar Shugaban Kasa Tinubu Sun Halarci Zaman Majalisar Dattawa

Shettima da Matar Shugaban Kasa Tinubu Sun Halarci Zaman Majalisar Dattawa

  • Majalisar dattawa ta 9 mai barin gado ranar Talata ta yi zaman bankwana a zauren majalisar ranar Asabar, 10 ga watan Yuni
  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da matar shugaban kasa, Remi Tinubu, sun halarci zaman
  • Yayin wannan zama na bankwana, an bai wa baki ɗaya Sanatocin shaidar aiki a bangaren masu doka a Najeriya

Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da matar shugaban ƙasa, Remi Tinubu, sun halarci zaman bankwana na majalisar dattawan Najeriya ta 9.

Channels tv ta ruwaito cewa a yau Asabar, 10 ga watan Yuni, majalisar dattawa ta yi zaman bankwana a zaurenta da ke birnin tarayya Abuja.

Shettima da Misis Tinubu.
Shettima da Matar Shugaban Kasa Tinubu Sun Halarci Zaman Majalisar Dattawa Hoto: Kashim Shettima, Remi Tinubu
Asali: Facebook

Shettima, shi ne Sanatan jihar Borno ta tsakiya mai barin Gado yayin da Remi Tinubu take wakiltar mazaɓar jihar Legas ta tsakiya har zuwa ranar da za'a rantsar da majalisa ta 10 ranar Talata.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Manyan Sarakunan Kasar Nan a Villa, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Wasu Kalamai

Ku sa kishin kasa a gaba - Shettima

A jawabinsa, mataimakin shugaban kasa ya ƙarfafa zababbun Sanatocin majalisar dattawa ta 10 mai zuwa su sanya kishin ƙasa a gaba da komai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Misis Tinubu, a nata jawabin ta jaddada kalaman Shettima, inda ta tuna wa zaɓaɓɓun yan majalisar dattawa su sanya kudirin gina kasa a zuƙatansu fiye da burin ƙashin kansu.

Uwar gidan shugaban ƙasan ta ƙara da cewa gwamnatin mai gidanta na buƙatar gogewa da kwarewar mambobin majalisa masu barin gado nan da ranar 13 ga watan Yuni.

Abubuwan da suka gudana a zaman bankwanan majalisa

Daga nan sai shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya dakatar da Oda 12 domin baiwa waɗanda suka halarci zaman bankwanan damar shigowa cikin zauren.

Magatakardan majalisar ya miƙa takardan shaidar aiki a ɓangaren masu dokoki ga shugaban majalisar dattawa da kuma mataimakinsa, Sanata Ovie Omo-Agege.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Muhimman Kalaman da Gwamnonin G5 Suka Faɗa Wa Shugaba Tinubu Sun Bayyana

Bayan nan, Sanata Lawan ya bai wa kowane Sanata takardar shaidar aikin majalisa, kamar yadda Punch ta rahoto.

Omo-Agege, ya fara isar da sakon bankwana da fatan Alheri, inda ya tuna shekaru huɗu da majalisa ta 9 ta shafe da kuma nasarorin da ta cimma.

Ya kuma roƙi Sanatocin da zasu sake dawowa a wani zangon su goyi bayan ɗan takarar da jam'iyyar APC a zaɓa a matsayin shugaban majalisar tarayya ta 10.

Gwamna Ya Nada Mace a Matsayin SSG

A wani labarin kuma kun ji cewa gwamnan jihar Ebonyi naɗa mace a matsayin Sakatariyar gwamnatin jihar karo na farko a tarihi.

Rahoto ya nuna cewa gabanin naɗa ta SSG, Farfesa Grace Umezurike, lakcara ce a jami'ar jihar Ebonyi da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel