Majalisa Ta 10: Kungiyar Kiristoci Ta Goyi Bayan Tsohon Gwamnan Arewa, Ta Bayyana Dalilai

Majalisa Ta 10: Kungiyar Kiristoci Ta Goyi Bayan Tsohon Gwamnan Arewa, Ta Bayyana Dalilai

  • Kungiyar Kiristoci ta CON ta goyi bayan zaban tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul'azizi Yari a matsayin shugaban majalisar dattawa
  • Yari yana daya daga cikin wadanda suka nuna sha'awarsu ta tsayawa takarar shugabancin majalisar
  • Kungiyar ta bayyana haka ne yayin wani babban taronta a ranar Alhamis 8 ga watan Yuni a Abuja

FCT, Abuja - Kungiyar Taron Fastoci da Limaman Kiristoci (CON) ta amince da zabin Abdulaziz Yari a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10.

Kungiyar ta bayyana haka ne yayin wani babban taronta a ranar Alhamis 8 ga watan Yuni a Abuja, inda ta ce Yari ya na da kwarewar zama shugaban majalisar.

Kungiyar Kiristoci ta goyi bayan Yari kan shugabancin majalisar dattawa
Majalisa Ta 10: Abdulaziz Na Daga Cikin Masu Neman Kujerar Majalisar. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Blessing Fashola, shugabar majami'ar Celestial ta ce bai kamata a zabi Kirista a wannan kujera ba inda ya kara da cewa kungiyar ba ta ga wanda ya cancanta ba kamar Yari.

Kara karanta wannan

Ko Gezau: Maryam Abacha Ta Ce Ba Ta Kewar Fadar Shugaban Kasa, Ta Koka Yadda Mutane Ke Muzanta Mijinta

A bar batun bangaranci ko addini ba, Yari ne mafi cancanta

A cewarta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A wannan majalisar ne ya kamata a yi magana daya da za ta hada kan 'yan kasa, duk wani abu da zai kawo rikicin addini da kabilanci ko bangaranci dole a yi watsi da shi."

Bayan duba dukkan 'yan takarar, ba tare da duba bangaranci ba ko addini ba, mun amince da Yari wanda shi yafi kowa cancanta a cikinsu, cewar TheCable.

Ta kara da cewa:

"CON ba ta siyasa ba ce amma ba ta amince da zabar Kirista a matsayin shugaban majalisar ba, saboda babu Kirista daga cikinsu da ya kai Yari cancanta.
"Ya kamata mu gane cewa a yanzu abin da kasar ke bukata shi ne shugabanni masu kwarewa ba tare da duba bangarensu ko addini ba.
"Kwarewar Yari ta nuna dacewarsa kan shugabancin majalisar, mutumin da yake da tunanin kawo ci gaba mai dorewa a kasar.

Kara karanta wannan

Zabe Saura Kwana 5, Shugaban kasa Ya Gagara Shawo Kan Zababbun ‘Yan Majalisa

"Ya nuna kwarewarsa a bangarori da dama da kuma dinke baraka a inda aka samu banbance-banbance."

Fashola ya ce wannan dama ce ta Arewa maso Yamma

Rahotanni sun ce Fashola ya bayyana cewa Arewa maso Yamma ce ya kamata a ba wa wannan dama ta shugaban majalisar dattawa ta 10.

Mambobi 67 Na Bayan Yari, Abdul Ningi Ya Ce Dole a Bar ’Yan Majalisa Su Zabi Son Ransu

A wani labarin, Sanata Abdul Ningi ya bayyana cewa kaso da yawa daga cikin 'yan majalisar dattawa na goyon bayan Abdulaziz Yari.

Ningi ya bayyana cewa mambobi 67 ne ke goyon bayan Abdulaziz Yari don tabbatar da shi a matsayin shugaban majalisar ta 10.

Asali: Legit.ng

Online view pixel