Sabon Gwamna Ya Tona Yadda Tsohon Gwamnan APC Ya Sulale da Motoci 17 da Kayan Ofis

Sabon Gwamna Ya Tona Yadda Tsohon Gwamnan APC Ya Sulale da Motoci 17 da Kayan Ofis

  • Dauda Lawal Dare ya jefi Bello Muhammad Matawalle da yi wa gidan gwamnatin Zamfara kar-kaf
  • Sabon Gwamnan jihar Zamfara ya ce wanda ya gada a mulki ya dauke motocin da ke aiki a ofishinsa
  • Gwamna Dare ya yi Allah-wadai da Matawalle, amma bai nuna zai karbo kayan da aka dauke ba

Zamfara - Dauda Lawal Dare wanda ya karbi mulkin jihar Zamfara, ya zargi Bello Muhammad Matawalle da barin gidan gwamnati da kayan al’umma.

A ranar Alhamis Daily Trust ta rahoto Gwamna Dauda Lawal Dare ya na cewa Bello Muhammad Matawalle ya dauke motoci da kayan aiki da zai bar ofis.

A ranar 29 ga watan Mayu aka rantsar da Dauda Dare a matsayin sabon Gwamnan jihar Zamfara.

Sabon Gwamna
Bello Matawalle a lokacin mulki Hoto: koko.ng
Asali: UGC

Da aka yi magana da shi a gidan rediyon Vision FM da ke garin Gusau, sabon gwamnan ya ce babu abin da ya gada a baitul-malin Zamfara illa bashi.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Rantsar da Wasu Kwamishinoninsa Kwanaki 2 da Hawa Karagar Mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dare ya ce kafin Gwamna Matawalle ya bar ofis, sai da ya tattara motoci 17 da ake da su a ofishin Gwamna da ofishin Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara.

Sannan Gwamnan ya ce ya iske an yi gaba da talabijin da na’urar dafa abinci da AC da kuma firji daga gidan gwamnati kafin rantsar da sabuwar gwamnati.

Jawabin Gwamna Dauda Lawal Dare

“Tsohon Gwamna Bello Matawalle ya tafi da motoci 17 daga ofishinsa da na mataimakin gwamna, yana cewa motocin mallakarsa ne.
Kai har kayan aiki na cikin ofis ba a kyale ba. Ta’adin da aka tafka ya wuce tunani, ban taba ganin rashin sanin ya kamata irin wannan ba.
Amma idan aka yi tsari da kyau, ina mai tabbatarwa mutanen jihar Zamfara cewa za mu yi bakin kokarinmu wajen gyara kura-kuran.

- Dauda Lawal Dare

Jaridar ta nemi jin ta bakin Zailani Bappa wanda shi ne Mai magana da yawun bakin Bello Matawalle, amma duka wayoyinsa na kashe a lokacin.

Kara karanta wannan

Ba a Ba Ni Mukamin Komai ba Inji Wanda Ake Cewa Ya Zama Kakakin Shugaban Kasa

Matawalle ya zama Gwamna ne a sakamakon rusa nasarar APC da kotu tayi a 2019, ya bar mulki bayan shekaru hudu a dalilin rasa tazarcen da ya yi.

Tinubu ya nada mukamai?

Jagora a APC, Femi Fani Kayode ne ya fara yada cewa Bola Tinubu ya yi nade-naden mukamai, a karshe mun kawo rahoto cewa labaran na karya ne.

Nadin da ake cewa sabon shugaban kasa ya yi ba gaskiya ba ne. Dele Alake ya tabbatar da haka, shi ma Segun Dada bai ce an ba shi mukami ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel