Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wakilan Amurka, Birtaniya Da Saudiyya, Ya Yi Wani Muhimmin Alkawari

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wakilan Amurka, Birtaniya Da Saudiyya, Ya Yi Wani Muhimmin Alkawari

  • Sabon shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya tabbatarwa al’ummar ƙasar nan ƙudirinsa na ganin ƙasar ta ci-gaba da kuma haɗin kan 'yan ƙasar
  • Bayan rantsar da shi a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, wakilan ƙasashen Birtaniya, Amurka, Saudiyya, da sauransu sun gana da Tinubu domin nuna goyon baya da kuma neman ƙara ƙulla alaka da Najeriya
  • Tinubu, bayan ganawa da wakilan, ya tabbatar da cewa ƙasar ba za ta wargaje ba, za ta tsayu kyam, ba tare da tangarda ba

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu a Abuja, ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Najeriya na 16 tare da shan alwashin cewa ƙasar ba za ta wargaje ba.

A jawabinsa na farko a dandalin Eagle Square, Tinubu ya kuma bayyana matakan da zai ɗauka domin ɗora kasar nan kan turbar bunkasar tattalin arziki, kwanciyar hankali da wadata.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rudani Yayin Da Rahoto Ya Yi Ikirarin Tinubu Ya Yi Nade-Naden Farko Bayan Rantsarwa

Tinubu ya gana da wakilan Amurka, Birtaniya da Saudiyya
Shugaba Tinubu ya fada ma wakilan Amurka, Birtaniya da Saudiyya cewa Najeriya ba za ta wargaje ba. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Ƙasashen sun taya murna da nuna goyon baya

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa jim kaɗan bayan rantsar da shi, shugaban ya gana da wakilai daga ƙasashen Birtaniya, Amurka, Saudiyya, Japan, Brazil, Koriya ta Kudu, Isra'ila, Cape Verde, Somalia da Nicaragua a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton The Cable ya ƙara da cewa jami’an diflomasiyyar sun gabatar da saƙon fatan alheri da kuma wasiƙun goyon baya da haɗin kai ga Tinubu.

‘Yan Najeriya sun yi tir da cire tallafin mai da Tinubu ya yi, sun ce Dangote ba zai sauƙaƙa farashin ga 'yan Najeriya ba

Cire tallafin man fetur da shugaba Bola Tinubu ya sanar a ranar rantsar da shi ya janyo cece-kuce daga ‘yan Najeriya.

‘Yan Najeriya dai sun ce ba a yi tunanin abinda cire tallafin man fetur ɗin ka iya jawowa ba, kuma babu wani shiri da gwamnati ta yi domin daƙile hakan.

Kara karanta wannan

Rantsar Da Tinubu: Datti Baba-Ahmed Ya Dau Zafi, Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya

Shugaban wani dandalin jama'a BudgIT, Seun Onigbinde, ya ce bai kamata gwamnati ta cire tallafin ba ba tare da ta rage yawan kashe kuɗaɗe da ake a gwamnatance ba.

Shugaban NNPC ya goyi bayan cire tallafin mai

A wani labarin mai alaƙa da wannan, shuganaban kamfanin NNPC na ƙasa, Mele Kyari ya bayyana goyon bayansa kan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi a yayin bikin rantsar da shi.

Tinubu ya bayyana cewa babu batun tallafin mai a cikin kasafin kuɗi na shekara ta 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng