NNPP Ta Yi Bayani Kan Rade-Radin Da Ake Na Komawar Kwankwaso APC

NNPP Ta Yi Bayani Kan Rade-Radin Da Ake Na Komawar Kwankwaso APC

  • Jam'iyyar NNPP ta yi watsi da raɗe-raɗin da ake yi na cewa ɗan takararta na shugabancin ƙasa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso zai koma jam'iyyar APC
  • Sakataren jam'iyyar ta NNPP na ƙasa, Dakta Major Agbo ne ya bayyana hakan, ranar Asabar a wani taro na manema labarai a Abuja
  • Ya ce babu wani aibu dangane da ganawar da Kwankwaso ya yi da Tinubu a birnin Paris na Kasar Faransa, saboda a cewarsa, Kwankwaso mutum ne na mutane

Abuja - A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne jam’iyyar NNPP ta kwantarwa da magoya bayanta hankali kan tunanin da suke na komawar ɗan takararta Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Jam'iyyar ta NNPP na mayar da martani ne dangane da ganawar da aka yi tsakanin Kwankwaso da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a Paris da ke ƙasar Faransa, jaridar The Punch ta yi rahoto.

Kara karanta wannan

Kotun Koli a Najeriya Ta Yanke Hukunci Kan Karar da PDP Ta Nemi a Soke Takarar Tinubu da Shettima

NNPP ta yi magana kan batun komawar Kwankwaso APC
Jam'iyyar NNPP ta ce Kwankwaso ba zai koma APC ba. Hoto: The Whistler NG
Asali: UGC

Ganawar ta Kwankwaso da Tinubu a Faransa ta janyo muhawara mai zafi a tsakanin al'umma, inda anan wasu suka fara raɗe-raɗin cewa Kwankwaso zai koma APC.

Kwankwaso mutum ne na mutane

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dakta Major Agbo, a wani taron manema labarai a Abuja, ya tabbatarwa da 'yan jam’iyyar cewa babu wani aibu a cikin haɗuwar ta Kwankwaso da Tinubu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana Kwankwaso a matsayin dan siyasar da yake da mutane a ko ina ba tare da la'akari da bambancin siyasa ko addini ba.

A cewar sa:

“Ba na so ku ji tsoron cewa zai tafi wani wuri. Babu inda zai je. Kamar yadda na faɗa, shi mutum ne mai mutane a kowace jam'iyya ta siyasa. Za ku ga irin hakan da dama a gaba.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bola Tinubu Ya Sanya Labule Da Tsohon Firaministan Burtaniya, Bayanai Sun Fito

Ya kuma ce nasarar zaɓen gwamnan jihar Kano da Abba Kabir, da mataimakinsa Aminu Gwarzo suka samu za ta haifar da sabon yanayi.

A halin da ake ciki, hadiman Tinubu da na Kwankwaso sun bayyana kwarin guiwar ƙawancen da aka samu tsakanin shugabanninsu.

Sun bayyana cewa hakan na nuni da yadda ya kamata a ce gwamnatin haɗaka ta kasance.

Wannan dai na zuwa ne tun bayan haɗuwar zaɓaɓɓen shuganaban ƙasar da Kwankwaso a birnin Paris da ke Faransa.

Batun ci-gaban ƙasa Tinubu ya tattauna da Kwankwaso

Ɗaya daga cikin tsofaffin 'yan gidan siyasar Tinubu, kuma tsohon darakta-janar na yaƙin neman zaɓensa, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce babu batun komawar Kwankwaso APC.

Jibrin wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa NNPP kuma ya yi nasarar lashe zaɓen majalisar wakilai, ya ce Tinubu da Kwankwaso sun gana ne domin tattauna yadda za su yi aiki tare domin haɗin kai da ci-gaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Kulla-Kullar Dawo Da Ahmed Lawan a Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa Ta 10

A wani rahoto na The Cable, ana tunanin cewa Bola Tinubu zai bai wa Kwankwaso mukamin minista a gwamnatinsa ta hadaka da yake shirin gudanarwa.

Kwankwaso ya tabbatar da cewa ya gana da Tinubu

A labarinmu na baya mai alaƙa da wannan, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya tabbatar da cewa ya gana da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu a Faransa.

Wasu na raɗe-raɗin cewa Bola Tinubu ya yi wa Kwankwaso tayin kujerar minista a yayin ganawar da suka shafe sama da sa'o'i huɗu suna yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel