"Za A Sha Jar Miya": Yan Najeriya Da Kansu Za Su Roƙi Tinubu Ya Yi Tazarce, Betta Edu

"Za A Sha Jar Miya": Yan Najeriya Da Kansu Za Su Roƙi Tinubu Ya Yi Tazarce, Betta Edu

  • Shugabar mata ta jam'iyyar APC ta ƙasa Dakta Betta Edu, ta ce 'yan Najeriya da kansu za su roƙi Tinubu ya sake fitowa takara bayan kammala shekaru huɗunsa na farko
  • Ta bayyana hakan ne dai a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels ya yi da ita jiya Alhamis
  • Ta kuma ce zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya gama tsara duk abubuwan da yake so ya cimmawa a kwanaki 60 ɗinsa na farko da zarar ya karɓi ragamar mulki

Shugabar mata ta jam’iyyar APC ta ƙasa, Dakta Betta Edu, ta ce ‘yan Najeriya za su roƙi Bola Tinubu, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ya sake tsayawa takara a karo na biyu bayan ya gama shekaru hudunsa na farko yana mulki.

Da take magana ranar Alhamis a wata hira da gidan talbijin na Channels, Edu ta ce Tinubu ya shirya tsaf domin fara aiki da zarar ya ɗare kujerar mulki.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Kunyata 'Yan Najeriya Ba," Tinubu Ya Faɗi Kalamai Masu Jan Hankali Bayan Buhari Ya Masa Abu 1

Betta Edu ta ce 'yan Najeriya sai sun roki Tinubu ya dawo a karo na biyu
Betta Edu ta ce 'yan Najeriya sai sun roki Tinubu ya dawo a karo na biyu. Hoto: @edu_betta
Asali: Twitter

Tinubu zai ɗora daga inda Buhari ya tsaya

Betta Edu ta kuma ce tsohon gwamnan na Legas zai yi aiki ne a kan abinda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado ba ta samu damar yi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce akwai buƙatar duk gwamnatin da ta karɓi mulki ta ɗora a kan ayyukan da gwamnatin baya ta fara ba ta samu damar ƙarisawa ba.

A kalamanta:

"Na yi imani da cewa 'yan Najeriya za su roƙi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bayan shekaru hudunsa, ya dawo a karo na biyu."
“Abu na farko da ya kamata mu fahimta shi ne, aiki a Najeriya aiki ne da ake buƙatar wani ya ci-gaba. Idan kun saurari jawabin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi a yau a ɗakin taro na gidan gwamnati, ya yi bayani ƙarara cewa ya yi ƙoƙari sosai a mulkinsa.”

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tura Wani Dattijo Gidan Yari Saboda Sarrafa Kwandala Da Ficika Zuwa Kayan Ado A Kano

"Ya ce yana fatan zai miƙa Najeriya ga wanda ya yi imanin zai ci-gaba daga inda ya tsaya kuma ya yi abinda ma ya fi nasa."

Tinubu ya gama tsara abubuwan da zai yi a kwanaki 60 na farko a ofis

Wani tsohon kwamishinan jihan Kuros Ribas, ya ce Tinubu yana da rubutattun shirye-shiryen abubuwan da zai gudanar a kwanaki 60 ɗinsa na farko a ofis, in ji rahoton The Cable.

Betta Edu ta kuma ƙara da cewa, Tinubu mutum ne mai nazari da zurfin tunani wanda yanzu haka ta tabbatar da ya gama shirya abubuwan da yake son ya fara gabatarwa da zarar ya amshi mulki.

A cewarta:

“Idan kun san Asiwaju Bola Tinubu, shi mutum ne mai zurfin tunani kuma ma'aikaci. Kuma gwani ne a wajen nazari da kuma dabaru.”
“Zan iya faɗa muku gaba gaɗi cewa, Tinubu ya riga da ya gama tsara abubuwan da yake fatan yi da kuma abubuwan da yake fatan cimmawa a cikin kwanaki 60 masu zuwa, haka nan a wane mataki da kuma a wane wuri.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bola Tinubu Ya Sanya Labule Da Tsohon Firaministan Burtaniya, Bayanai Sun Fito

“Ya riga da ya fahimci duk aikin da ke gabansa sosai. Ya shirya tsaf. Yana so ya fara aiwatar da ayyuka.”

A ranar 29 ga watan Mayu ne dai ake sa ran za a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu.

Ɓangarori bakwai da ake neman Tinubu ya kawo gyara

A wani labarinmu na baya, kun karanta ɓangarori guda bakwai da 'yan Najeriya ke fatan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kawo gyara a cikinsu.

Akwai ayyuka da dama da gwamnatin baya ta shugaba Muhammadu Buhari ta bari da ake fatan gwamantin Tinubu za ta ƙarisa su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel