Najeriya Zata Ƙara Bunkasa a Mulkin Bola Tinubu, Shugaba Buhari

Najeriya Zata Ƙara Bunkasa a Mulkin Bola Tinubu, Shugaba Buhari

  • Shugaba Buhari, ya bayyana cewa babu tantama Najeriya zata ƙara bunƙasa a karkashin mulkin Bola Tinubu
  • Buhari ya ce Yan Najeriya sun nutsu sun nuna wayewa wajen zaben wanda ya dace ya shugabance su a irin wannan lokacin
  • Ya yi waɗan nan kalamai ne a wurin karrama zababben shugaban kasa da lambar girmamawa ma fi daraja

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana yaƙinin cewa Najeriya zata ci gaba da bunƙasa karkashin shugabancin zababben shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Buhari ya yi wannan furuci ne a wurin bikin karrama Tinubu da lambar girmamawa mafi daraja GCFR a taƙaice da kuma karrama Kashim Shettima a Abuja.

Tinubu da Buhari.
Najeriya Zata Ƙara Bunkasa a Mulkin Bola Tinubu, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Channels tv ta ce a wurin taron wanda ya gudana a ɗakin taro na fadar shugaban kasa ranar Alhamis, Buhari ya faɗawa Tinubu cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗebo da Zafi, Ya Fallasa Masu Satar Dukiyar Talakawa a Kusa da Buhari

"Mutanen Najeriya sun gano kwarewarka a shugabanci, gogewar siyasa da kuma burin bautawa ƙasar nan shiyasa suka zaɓe ka suka ɗora maka nauyin shugabancin ƙasar da suke ƙauna."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Banda tantama Najeriya zata ƙara bunkasa kuma ta cimma matsayi mai girma a karkashin mulkinka. Ka fi kowa cancanta a cikin yan takarar da suka shiga zaɓe kuma 'yan Najeriya suka zakulo ka."

Shugaba mai barin gado ya ce tarihin abinda Bola Tinubu ya yi a matsayin gwamnan jihar Legas tsakanin 1999 zuwa 2007 ya isa ya nuna sadaukarwan zababben shugaban ƙasa domin jin daɗin al'umma.

A cewarsa, shugaba mai jiran gado mutum ne mai ƙaunar haɗin kan ƙasa kuma ya bayyana haka ƙarara a tarihin siyasarsa na baya.

Ƙasar nan na cikin kalubale - Buhari

Bugu da ƙari, Buhari ya ƙara tunawa Tinubu da Shettima cewa ƙasar nan tana fuskantar kalubale masu yawa, don haka akwai bukatar su zage dantse da zaran sun karbi mulki ranar Litinin mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Kunyata 'Yan Najeriya Ba," Tinubu Ya Faɗi Kalamai Masu Jan Hankali Bayan Buhari Ya Masa Abu 1

Ranar 29 ga watan Mayu, 2023, shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, zai koma gefe ya miƙa wa Bola Tinubu ragamar mulki.

Ana cin hanci a Villa - Ortom

A wani labarin kuma Gwamna Ortom Ya Debo da Zafi, Ya Tona Masu Cin Hanci a Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnan ya kuma yi ikirarin cewa fadar shugaban kasa ce ta kulla makirce-makircen da suka sa ya sha ƙasa a zaben Sanata 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel