Gyaran Hali: Kotu Ta Umarci a Zane Wani Matashi Barawon Kaji Da Ransu Bulali 8 a Kaduna

Gyaran Hali: Kotu Ta Umarci a Zane Wani Matashi Barawon Kaji Da Ransu Bulali 8 a Kaduna

  • Kotun magistare ta umarci da a zana wani matashi da ake zargin ya saci kaji 8 da ransu a Kawo cikin Kaduna
  • Wanda ake zargin ya saci kajin ne da ransu yayin da ya saka a buhu ya yi kokarin tserewa kafin a kama shi
  • An yanke hukuncin ne a yau Laraba 24 ga watan Mayu a kotun da ke zamanta Kaduna babban birnin jihar

Jihar Kaduna - Kotun magistare da ke zamanta a Kaduna ta umarci da a hukunta wani wanda ake mai suna Adamu Isah da bulali takwas saboda satar kaji masu rai guda 10.

An yanke wannan hukuncin ne a ranar Laraba 24 ga watan Mayu a kotun da ke Kaduna babban birnin jihar Kaduna.

Kotu a Najeriya
Kotu Ta Umarci a Zana Matashi Barawon Kaji Bulali 8 a Kaduna. Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Mai shari’a, Ibrahim Emmanuel ya gargadi wanda ake zargin da kaucewa aikata laifuka, sannan ya zamto mutum na gari daga wannan ranar.

Kara karanta wannan

Saura Kwana 6: Na Matsu Na Gama Mulkina Saboda Matsin Lamba, Buhari Ya Koka Kan Yawan Tarurruka

Isah ya amince da laifukan da ake zarginsa

Wanda ake karar ya tabbatar da aikata laifukan da ake tuhumarsa akansu na wuce gona da iri da kuma sata inda ya roki kotun da ta masa sassauci, yayin da ya yi alkawarin zama mutumin kirki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

The Times ta tattaro cewa ana zargin Isah da laifuka da suka hada da hada kai wurin aikata laifi da wuce gona da iri da kuma sata, cewar Punch.

Sani Rabiu ya shigar da kara

Tun farko, mai gabatar da kara, Chidi Leo ya fadawa kotu cewa Sani Rabiu ya kai kara akan lamarin a ofishin ‘yan sanda na Gabasawa a ranar 13 ga watan Mayu.

Ya ce wanda ake zargin da wasu mutane biyu sun hada baki suka sace kaji masu rai guda 10 daga gonar kiwon kajin da ke Kawo.

Kara karanta wannan

An Daure Lakcara Shekaru 5 a Gidan Kaso Bisa Zargin Sama da Fadi da N6m Na Tallafin Karatunsa

Leo ya kara da cewa wanda ake zargin ya yi kokarin guduwa da kajin a cikin buhu yayin da aka kama shi amma sauran abokan nashi har yanzu ba a san inda suke ba.

Mai gabatar da karan ya ce abin da suka aikata ya sabawa sashi na 308 da 233 da kuma 217 na dokokin jihar Kaduna na shekarar 2017.

Kotu Ta Datse Igiyar Auren Fasto Saboda Yawan Jibgar Matarsa, Ta Mallaka Wa Matar Kadarorinsa

A wani labarin, kotu da ke zamanta a jihar Edo ta datse auren wani Fasto bisa zargin cin zarafi da jibgar matarsa.

Faston mai suna Oni Muyiwa ya saba cin zarafin matar tasa da kuma yawan sakin mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.