Na Rantse Ban Saci Ko Kobo Ba Daga Lalitar Jihar Kaduna, In Ji Gwamna El-Rufai

Na Rantse Ban Saci Ko Kobo Ba Daga Lalitar Jihar Kaduna, In Ji Gwamna El-Rufai

  • Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce bai taɓa ɗaukar ko kobo ba da ba nasa ba daga lalitar gwamnatin jihar
  • Ya kuma ce bai kwashe kuɗaɗe domin ya je ya gina gidaje ba, hasali ma har yanzu gidansa ƙwara ɗaya ne tak
  • Ya kuma ce duk gwamnan da ya ke ganin cewa bai saci ko sisin kobo a lalitar ba da ya zo ya rantse da alƙur'ani

Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce bai taɓa satar dukiyar al’umma ba a tsawon wa’adinsa biyu na mulki da ya yi.

Ya bayyana hakan ne a ƙarshen makon da ya gabata, a lokacin da yake jawabinsa na ƙarshe a matsayin gwamna.

Daily Trust ta ruwaito cewa El-Rufai zai miƙawa zaɓaɓɓen Gwamnan Kaduna Uba Sani mulki a nan da mako guda mai zuwa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Tayar Masa Da Hankali Lokacin Zabe

El-Rufai ya ce shi ba barawo bane, bai taba satar kudin jama'a ba
Malam Nasiru El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna | Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Zan iya rantsewa cewa ban taɓa sata ba

El-Rufai dai ya yi wannan batu ne a yayin da yake maida martani ga masu sukarsa kan al'amuran mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa zai iya rantsewa kan cewa shi bai taɓa satar sisin kobo daga lalitar gwamnati ba a lokacin da yake kan mulki.

"Zan iya rantsewa cewa ban taɓa satar ko kobo a cikin asusun gwamnati ba,"

El-Rufai ya ƙara da cewa gidan daya gina tun kafin ya zama gwamna shi ne wanda zai yi ritaya idan wa’adin mulkinsa ya ƙare a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Ya kuma ce shi bai karɓi kuɗi ya je ya gina katafaren gida ko ya gudu Dubai da su ba kamar yadda wani ya yi.

Gida na guda ɗaya ne tak bani da wani

Kara karanta wannan

Ba Sassauci: Yana Dab Da Sauka Mulki, Gwamna El-Rufai Ya Sha Wani Muhimmin Alwashi

El-Rufai ya kuma ce gidan da dai aka san yana da shi tun kafin hawansa mulki shi ne dai ya ke ciki har yanzu, bai gina wani ba.

Yace:

“Na zama gwamnan Kaduna da gida ɗaya a kan titin Danja da ke Ungwan Sarki. Yanzu na gama cikin godiyar Allah, shine kaɗai gidan da nake da shi. Ban gina wani katafaren gida ba, bana bukata.”

The Nation ta wallafa cewa El-Rufai ya kuma bugi ƙirjin cewa shi bai taɓa ko sisi ba, kuma yana ƙalubalantar duk wani gwamna da ya mulki Kaduna a baya da ya zo ya rantse da Ƙur'ani kan cewa bai saci kuɗin jihar ba.

Yan Shi'a sun caccaki gwamna El-Rufai

A wani labarin na daban, yan ƙungiyar IMN waɗanda aka fi sani da 'yan Shi'a sun caccaki gwamna Nasir El-Rufai dangane da rushe musu wasu gine-gine.

Sun bayyana cewa ba a bi ƙa'ida ba wajen aiwatar da shirin rushe gine-ginen na su da aka fara jiya Lahadi a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel