Sarkin Musulmi: Babu Wanda Zai Iya Hana Rantsar Da Tinubu

Sarkin Musulmi: Babu Wanda Zai Iya Hana Rantsar Da Tinubu

  • Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce ko suna so ko basa so sai an rantsar da Bola Tinubu
  • Ya roƙi 'yan Najeriya da su taya gwamnatin ta Tinubu da addu'a don samun damar gudanar da sha'anin mulki yadda ya kamata
  • Ya kuma yi kira ga shugabannin addinai da shuwagabanin gargajiya a kan su haɗa kawunansu don samun ci-gaban ƙasa baki ɗaya

Abuja - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya kira ga ‘yan Najeriya da su yi wa gwamnati mai zuwa addu’a don samun nasarar tafiyar da al’amuran ƙasar yadda ya kamata.

Sultan ya bayyana haka a yayin wani taron tattaunawa da sarakunan gargajiya da na addinai ranar Laraba a Abuja, kamar yadda ya ke a rahoton Daily Trust

sultan
Sarkin Musulmi Ya Ce Babu Wanda Zai Iya Hana Bikin Rantsar Da Tinubu. Hoto: Arise TV
Asali: UGC

Ya ce ya kamata kowa ya sani cewa sabuwar gwamnati za ta karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayu ko suna so, ko basa so.

Kara karanta wannan

“Shugabannin Ƙasa 120 Za Su Halarci Bikin Rantsar Da Tinubu": Cewar Adamu Garba, Jigo a Jam'iyyar APC

Ku ci-gaba da ƙoƙarin da kuke yi kan batun yaƙi da auren wuri

Taron wanda bankin duniya ya shirya don samar da hanyoyin bunƙasa rayuwar al'ummar ƙasar nan, musamman ma dai batun ilimin yara mata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma yi kira ga mahalarta taron da kada su daina ƙoƙarin da suke na kawo karshen auren wuri da sauran abubuwan da ke daƙile ci-gaban 'ya 'ya mata a yankunansu

A cewarsa:

“Dole ne a samu sauyi, domin nan da ‘yan kwanaki ko makonni kaɗan, za a samu sabuwar gwamnati, me za mu yi don ganin gwamnatin ta daidaita?”
"Ko mutum ya na so ko ba ya so, dole ne a rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu, don haka ba mu da abinda za mu iya yi banda addu'a saboda mun yi imani da cewa Allah madaukakin sarki ne ke da ikon bayarwa da hanawa.”

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Yana Landan, Osinbajo Ya Amince a Kafa Sababbin Jami’o’i 36 a Najeriya

Sarakuna da malamai su haɗa kai don ci-gaban ƙasa

Ya kuma ƙara da cewa wannan dama ce ga shugabannin addinai da na gargajiya, su haɗa kawunansu wajen ciyar da ƙasar gaba.

Ya kuma ce a matsayinsu na shugabannin addinai da na gargajiya, dole ne su yi kira a yi adalci a kan duk abubuwan da za a gudanar.

Atiku ya soki kiran wayar Blinken da Tinubu

A wani labarin na daban kuma, Alhaji Atiku Abubakar ya soki kiran wayar da ya wakana tsakanin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da Bola Tinubu.

Atiku ya yi zargin cewa kiran wayar na nufin amincewar Amurka da maguɗin zaɓen da aka yi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel