Tinubu Ba Zai Manta Ganduje, El-Rufai, Sauran Gwamnonin Arewa a Rabon Mukamai ba

Tinubu Ba Zai Manta Ganduje, El-Rufai, Sauran Gwamnonin Arewa a Rabon Mukamai ba

  • Bola Tinubu zai yi sakayya ga Gwamnonin APC masu barin-gadon mulki da suka taimaka masa
  • Bayo Onanuga ya ce zababben shugaban na Najeriya ba zai kyale wadannan Gwamnoni haka ba
  • Da ya zanta da manema labarai, na-kusa da Tinubun ya yi bayanin shirin Gwamnati mai zuwa

Abuja - A wata hira ta musamman da aka yi da Bayo Onanuga, wanda yana cikin kwamitin karbar mulkin Najeriya, ya yi bayanin muhimman batutuwa.

Jaridar Daily Trust ta zanta da Bayo Onanuga a kan abubuwan da suka shafi siyasa, zaben 2023, gwamnati mai zuwa da kuma shirye-shiryen Bola Tinubu.

Darektan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben APC ya ce a cikin kwanaki goma na farko, Bola Tinubu zai sanar da wadanda za su zama hadimansa.

Bola Tinubu
Bola Tinubu zai bar Najeriya Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Onanuga ya ce zuwa kasar waje da zababben shugaban kasar ya yi, zai ba shi damar tunanin yadda zai kafa gwamnati ba tare da mutane sun hana shi sakat ba.

Kara karanta wannan

Yawaita Zuwa Turai: Tinubu zama zai yi ya mulki Najeiya, inji hadiminsa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A hirar, an fahimci cewa babu tabbacin a kwanakin farko za a fitar da sunayen Ministoci, amma Onanuga ya nuna za a nada su zuwa lokacin da aka tsaida.

‘Dan siyasar ya kuma tabbatar da mai gidansa ba zai ci amanar wadanda suka taimake shi ba.

Ramawa kura aniyarta

Idan tsohon Gwamnan na Legas ya shiga ofis, Onanuga ya ce zai ba duk Gwamnonin APC na jihohin Arewa masu barin-gado mukamai a gwamnatin tarayya.

Nasir El-Rufai, Abdullahi Ganduje, Aminu Masari, Badaru Abubakar, Abubakar Sani Bello, Abubakar Bagudu za su sauka daga mulki a karshen Mayun nan.
"Ka da in yi wa zababben shugaban kasa gaggawa. Amma duka mutanen da aka fada su na da kusanci da shi, sun taimaka masa wajen samun mulki.
Har a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC sun taimake shi, ban san me ya yi masu tanadi ba.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu: Kashim Shettima Ta Faɗi Kuskuren da Shugaba Buhari Ya Tafka a Mulkinsa Kamar Na Jonathan

- Bayo Onanuga

Simon Lalong fa?

Gwamna Simon Lalong shi ne Darekta Janar na yakin neman zabe, saboda haka duk su na nan. Na tabbata zai san amfannin da za su yi masa a gwamnati.
Ba zai iya watsi da su ba domin dukkansu sun taka rawar gani wajen yakin neman zabensa.

- Bayo Onanuga

Mista Onanguga yana ganin babu mamaki ayi amfani da majalisa a tsige Godwin Emefiele, sannan bai da masaniya ko za a ba irinsu Nyesom Wike mukami.

Zaben majalisar tarayya

A baya rahoto ya zo cewa Abdul'aziz Yari, ya ziyarci jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa a Abuja domin samun goyon baya a majalisa.

An kuma fahimci Sanata Rufai Hanga ya na fafutuka domin Kawu Sumaila ya samu shugabancin marasa rinjaye a Majalisar dattawa saboda a taimaki Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel