"Rayuwa Kenan": Tsaffin Hotunan Ekeremadu Tare Da Sarki Charles III Ya Janyo Muhawara A Intanet

"Rayuwa Kenan": Tsaffin Hotunan Ekeremadu Tare Da Sarki Charles III Ya Janyo Muhawara A Intanet

  • Hotunan sarki Charles III da tsohon mataimakin kakakin majalisar dattawa Ekweremadu sun janyo hankulan jama'a a kafafen sadarwa
  • A hoton an ga tsohon Sanatan tare da Yariman Wales, wato Yarima Charles, a shekarar 2018, a wani taron cin abinci da ma'aikatar harkokin Birtaniya ta shirya a Abuja
  • An dai naɗa Sarki Charles III ne a ranar Asabar, 6 ga watan Mayu a cocin Westminster Abbey, a yayin da kuma a ranar Juma'a aka yanke ma Ekweremadu hukuncin ɗaurin shekaru 10 a magarkamar Landan

Wasu tsofaffin hotuna na tsohon mataimakin kakakin majalissar dokoki ta ƙasa Ike Ekweremadu tare da sabon sarkin ƙasar Birtaniya wato sarki Charles III sun jawo hankula a kafafen sada zumunta.

Hotunan dai waɗanda Ekweremadu ya wallafa a shafinsa na Tuwita an ɗauke su ne a watan Nuwamban shekarar 2018 a yayin wata liyafar cin abinci da ma'aikatar harkokin Birtaniya ta shirya ma su Yarima Charles a Abuja.

Kara karanta wannan

Kungiyar Ibo Ta Najeriya Ta Ragargaji Gwamnatin Buhari Kan Hukuncin Ekweremadu, Ta Bayyana Mataki Na Gaba

Ekweremadu
Sarki Charles III tare da Ike Ekweremadu a Abuja. Hoto: @iamekweremadu
Asali: Twitter

Yadda aka daure sanatan a Landan

Idan ba ku manta ba, a ranar Juma'a, 6 ga watan Mayu ne dai wata kotu da ke a Birtaniya ta yankewa Ike Ekweremadu hukuncin ɗaurin shekaru tara da watanni takwas a gidan yari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kuma kotun ta yankewa matar Ekweremadu, Beatrice, hukuncin ɗaurin shekaru huɗu da wata shida, a yayin da kuma likitan da ya taimaka musu mai suna Dakta Obinna Obeta ya samu hukuncin shekaru 10 daga kotun, gami da karɓe lasisin aikinsa.

Sai dai kuma Kayode Ajulo wani lauya masanin doka ya shaida ma Vanguard cewa akwai yiwuwar sabon sarkin ya iya yafe ma Ekweremadu laifin da ake tuhumarsa da shi.

Yan Najeriya sun yi sharhi a kafar sadarwa

Legit.ng ta tattaro muku yadda wasu 'yan Najeriya ke tofa albarkacin bakunansu kan wannan ƙangi da Ekweremadu ya tsinci kansa a ciki, duk kuwa da ganin da ake na cewar yana da kyakkyawar alaƙa da sabon sarkin.

Kara karanta wannan

Diyar Ekweremadu Sonia Ta Magantu Yayin da Kotun Birtaniya Ta Aika Iyayenta Magarkama, Bidiyo Ya Bayyana

Wani mai amfanin da shafin na Tuwita mai suna @AEbimomi ya ce:

"Zai je ya yi shekaru tara a gidan yarin ƙasar Ingila, duk da sanin da ya yi wa tsohon yarima wanda ya zama sarki a yanzu kuma mai iko akan gidajen yarin Birtaniya kuma duk a cikin sati ɗaya hakan ya faru. Wannan wace iriyar rayuwa ce.”

Wani mai suna @FrankyStarrz cewa ya ke:

“Wannan fa shine sarkin. Tare da ɗan Najeriya da aka yanke wa hukuncin shekaru tara. An same shi da aikata laifin safarar sassan jikin ɗan adam”

Wani mai amfani da kafar ta Tuwita kuma cewa ya yi:

“yanzu kuma ga ka a gidan yarin ƙasar shi.”

Hotunan nadin sarautar Sarki Charles III

A labarin mu na baya, mun kawo muku hotunan nadin sarautar Sarki Charles III wadanda suka karade ko wane lungu da sako na kafafen sada zumunta.

An dai gudanar da wannan nadin sarautar ne a ranar Asabar da ta gabata a cocin Westminster Abbey da ke a kasar Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel