Ba Za Ta Yi Wu ba: Gwamnan APC Zai Yaki Jam’iyya Kan ‘Rashin Adalcin’ Kason Majalisa

Ba Za Ta Yi Wu ba: Gwamnan APC Zai Yaki Jam’iyya Kan ‘Rashin Adalcin’ Kason Majalisa

  • Rotimi Akeredolu ya ce ba su yarda da Bola Tinubu a kan yadda aka yi rabon mukaman Majalisa ba
  • Gwamnan Ondo yana ganin an yi wa mutanen Arewa ta tsakiya rashin adalci duk da gudumuwarsu a APC
  • Idan aka tafi a haka, Gwamna Akeredolu yana ganin shugaban kasa mai jiran gado aka yi wa tarko

Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya nuna rashin amincewarsa ga yadda jam’iyyar APC ta yi kason yadda za a raba kujerun majalisar tarayya.

A wani jawabi da ya fitar, tashar Channels ta ce Gwamna Rotimi Akeredolu ya zargi jam’iyya mai mulki da rashin adalci da fifita yankin Arewa maso yamma.

Akeredolu ya na ganin ba ayi gaskiya da aka amince shugaban majalisar wakilai da mataimakin shugaban majalisar dattawa duk su fito daga yanki guda ba.

Kara karanta wannan

Ba a Haka: Inda Tinubu Ya Yi Kuskure Wajen Shugabancin Majalisar Dattawa – Sanata

Tinubu
Shugaban kasa mai jiran gado a Fatakwal Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar Gwamnonin Kudu maso yammacin Najeriyan ya yi mamakin yadda aka danne mutanen Arewa ta tsakiya saboda a fifita makwabtan su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A jawabin na sa, Daily Trust ta ce Mai girma Akeredolu bai kuma goyon bayan shugaban majalisar wakilai ya fito daga yankin Arewa maso gabashin kasar.

Aikin na kusa da Tinubu ne

Saboda haka la’akari da kusancin wasu na kusa da zababben shugaban kasa wajen kebe kujerun majalisar tarayya ya jawo an fara da rashin yarda da zargin juna.

Gwamnan yana ganin ya kamata jam’iyyar APC ta gujewa wannan ‘tarko’ da aka dana a tashin farko, a cewarsa hakan zai zama cikas ne ga mulkin Bola Tinubu.

"A fili yake cewa za a ba yanki daya fifiko a lamarin nan, Arewa maso yamma zai samu fifiko da shugabannin majalisa biyu a cikin hudu.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Arewa maso Yamma ta samu Shugabancin majalisar wakilai da dattawa a APC

Abin da hakan yake nufi shi ne yankin Arewa maso tsakiya ba za su samu kujera ko daya ba saboda shiru-shirunsu da biyayyar da suka nuna."

- Rotimi Akeredolu

Ina mafita?

An rahoto Gwamnan na Ondo yana zargin shugabannin jam’iyya da yin watsi da rawar ganin da Gwamnonin APC suka taka wajen nasarar da aka yi a 2023.

Akeredolu ya ce NWC tayi gaggawan daukar matsaya ba tare da zama da PGF da masu neman shugabancin majalisa, ya bada shawarar APC ta sake nazari.

Matsayar Sanatocin Ibo

Ifeanyi Ubah ya fito yana cewa babu yadda za ayi amfani da karfi wajen shugabancin majalisa alhali su Sanatoci mutane ne masu cin gashin kan su a dokar kasa.

An ji labari Sanatan na Anambra ya ce kyau a ce an yi zama da su an tattauna kafin a dauki matsaya, ya ce jam’iyyar APC mai mulki ba tayi abin da ya kamata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel