Bayan Shan Kaye, Dan Majalisar Tarayya Ya Koma Jam'iyyar PDP a Delta

Bayan Shan Kaye, Dan Majalisar Tarayya Ya Koma Jam'iyyar PDP a Delta

  • Ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Delta, Honorabil Ben Roland Igbakpa, ya koma jam'iyyar PDP bayan shan kaye a zabe
  • Alamu sun tabbatar da komawarsa jam'iyyar da ya fito bayan sunansa ya shiga kwamitin miƙa mulki ga sabuwar gwamnati
  • Honorabul Igbakpa ya yi zargin cewa daloli da Nairori ne suka kwace masa nasarar da ya samu a zaben fidda gwani

Delta - Mamban majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazabar Ethiope, jihar Delta, Honorabul Ben Roland Igbakpa, ya sake komawa gida jam'iyyar PDP.

Leadership ta rahoto cewa alamu sun nuna ɗan majalisar ya tattara kayansa ya koma PDP a makon da ya shige sa'ilin da aka ga sunansa ya fito baro-baro a kwamitin miƙa mulki.

Ben Roland Igbakpa.
Bayan Shan Kaye, Dan Majalisar Tarayya Ya Koma Jam'iyyar PDP a Delta Hoto: leadership
Asali: UGC

Bayan sunansa ya shiga kwamitin, maimakon ya karyata ko ya yi watsi da sagala shi a kwamitin, sai aka ga ɗan majalisar ya rungumin aikin kwamitin hannu bibbiyu.

Kara karanta wannan

Jiga-Jigan 'Yan Majalisa 5 Na APC Da Suka Lashi Takobin Yaƙar Ɗan Takarar Tinubu a Majalisa Ta 10

Da gaske ya koma jam'iyyar PDP?

Da yake tabbatar da batun sake komawa PDP, Honorabul Igbakpa, ya ce dama tun asali shi ya lashe zaben fidda gwani amma naira da dala suka masa fin karfi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce sakamakon nuna masa ba shi da galihu, shiyasa ya tattara kayansa ya koma jam'iyyar New Nigeria People’s Party, (NNPP) domin cika burinsa na shiga takara.

Yadda ya sha kaye a zaben fidda gwani

Ɗan majalisar wanda ke kan kujera yanzu haka ya fafata da ɗiyar tsohon gwamna, Chief James Ibori, Erhiatake Ibori-Suenu, amma karfi ya zo ɗaya a zaben fidda gwanin farko.

Bayan sakamakon zaben fidda gwanin farko ya nuna kowane daya daga cikin yan takarar biyu ya samu kuri'a 34, sai PDP ta ƙara shirya zabe na biyu kuma ɗan majalisar ya sha kaye.

Kara karanta wannan

Babba Jigon APC Ya Faɗi Gwamnan da Ka Iya Ficewa Daga PDP, Ya Ce Zasu Tarbe Shi Hannu Biyu a APC

Haka nan a babban zabe, yar takarar PDP watau ɗiyar Ibori ta samu kuri'u 10,634 ta lallasa dan majalisa mai ci, Igbakpa, ɗan takara a inuwar NNPP wanda ya tashi da ƙuri'u 3,591.

Wase Da Yan Takarar Shugabancin Majalisa 5 Sun Gana da APC NWC

A wani labarin kuma Jiga-Jigan Yan Majalisa 6 Masu Neman Shugabanci Sun Gana da Shugabannin APC

Mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayya, Idris Wase da wasu 'yan takarar kakakin majalisa 5 sun gana da Adamu, NWC-APC.

Wannan na zuwa ne bayan APC ta fitar da ɗan takarar da take goyon baya a majalisa ta 10. Wase, Doguwa da wasu yan takara sun lashi takobin yaƙar wanda Tinubu, APC ke so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel