Bola Tinubu Ya Roki Kotu Ta Shure Kar Jam'iyyar APM Kan Abu 1

Bola Tinubu Ya Roki Kotu Ta Shure Kar Jam'iyyar APM Kan Abu 1

  • Shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci Kotun zabe ta ƙori ƙarar jam'iyyar APM
  • A ranar Talata 9 ga watan Mayu, 2023, Kotun ta sake zaman sauraron kararrakin da ke kalubalantar nasarar Tinubu a zaɓen da ya wuce
  • APM na cikin kara biyu da Kotun ta saurara yau Talata amma daga baya ta ɗage zaman zuwa ranar Alhamis

Abuja - Rahoton Channels tv ya tattaro cewa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya roki Kotun zaɓe a Najeriya ta kori karar da jam'iyyar APM ta kalubalanci nasarar da ya samu.

A rana ta biyu ta sauraron korafe-korafen da suka shafi zaɓen shugaban kasa, APM ta shaida wa Kotu cewa ta cike Fam ɗin bayanan fara sauraron ƙara TF 008.

Tinubu.
Bola Tinubu Ya Roki Kotu Ta Shure Kar Jam'iyyar APM Kan Abu 1 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Lauyan shugaban kasa mai jiran gado, Akin Olujimi, ya shaida wa Alkalin cewa amsoshin da suka bayar a Fam ɗin na haɗe da rokon Kotu ta yi watsi da ƙarar.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Ɗage Saurarom Ƙarar Jam'iyyar Adawa 1, Ta Baiwa Tinubu, APC, INEC da Wasu 2 Umarni

Babban lauyan mai matsayin SAN ya ce karar da APM ta shigar ba ta dace ba ko kaɗan don haka ya kamata Kotu ta koreta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta ɗage karar zuwa ranar Alhamis

Bayan sauraron waɗannn jawabai daga ɓangarori biyu, Kotun zaben ta sanar da ɗage sauraron ƙarar APM zuwa ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu, 2023, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Shugaban kwamitin alkalan Kotun, mai shari'a Haruna Tsammani, wanda ya sanar da ɗage ƙarar, ya bukaci kowane ɓangare su tantance batutuwan da za'a tattauna a kansu.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda Kotu ke ci gaba da sauraron kararrakin zaɓen shugaban kasa yau Talata, 9 ga watan Mayu, 2023, bayan zaman farko ranar Litinin.

Kowane lokaci daga yanzu Tinubu zai iya fita Najeriya - Rahman

A wani labarin kuma Kun ji cewa Zababben Shugaban Kasa Ya Shirya Tafiya Ƙasar Waje Gabanin Ranar Bikin Rantsarwa

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Mai Jiran Gado, Bola Tinubu Zai Ƙara Tafiya Ƙasar Waje? Gaskiya Ta Bayyana

Mai magana da yawun shugaban kasa mai jiran gado, Tunde Rahman, ya tabbatar da cewa Bola Tinubu ya fara shirin rataya jakarsa zuwa wata ƙasar waje.

Rahotanni sun nuna cewa Tinubu zai sake fita daga Najeriya ne domin guje wa taƙaddamar da ka iya tasowa game da batun shugabancin majalisa ta 10.

Asali: Legit.ng

Online view pixel