Kotun Zabe Ta Dage Karar Jam'iyyar APM Zuwa Ranar Alhamis Mai Zuwa

Kotun Zabe Ta Dage Karar Jam'iyyar APM Zuwa Ranar Alhamis Mai Zuwa

  • Kotu ta ɗage sauraron ƙarar da jam'iyyar APM ta ta shigar don ta kalubalanci nasarar zababben shugaban kasa zuwa ranar Alhamis
  • Mai shari'a Haruna Tsammani ya bukaci APM da waɗanda ake tuhuma su zauna su fahimci juna kan abinda ke kunshe a ƙarar
  • A zaman jiya Litinin, Kotu ta kori ƙarar jam'iyyar AA kana ta ɗage guda biyu zuwa ranar Laraba, 10 ga watan Mayu

Abuja - Kotun sauraron karar zaben shugaban kasa mai zama a Abuja ta ɗage zaman sauraron karar da jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta shigar kan nasarar Bola Ahmed Tinubu.

Rahoton jaridar Daily Trsut ya tattaro cewa Kotun ta matsar da zaman sauraron ƙorafin APM zuwa ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu, 2023.

APM da Tinubu.
Kotun Zabe Ta Dage Karar Jam'iyyar APM Zuwa Ranar Alhamis Mai Zuwa Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Mai shari'a Haruna Tsammani, wanda ke jagorantar kwamitin alkalai 5, ya umarci jam'iyyar da waɗanda take tuhuma a karar, su tantance muhimman batutuwan dake ƙunshe a ƙarar gabanin ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Betara Ya Yi Fatali Da APC, Ya Nuna Sha’awarsa Ta Tsayawa Takara

Alkalin ya ƙara da cewa a zama mai zuwa ranar Alhamis, Kotu zata ƙayyade baki ɗaya korafe-ƙorafen dake cikin ƙarar domin gujewa bata lokaci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun da farko, jam'iyyar APM ta bakin lauyoyinta guda biyu, O.A. Atoyebi (SAN) da kuma S.A.T. Abubakar Esq, sun yi wa Kotu bayani kan waɗanda ake tuhuma a ƙarar.

Lauyoyin sun shaida wa Kotu cewa jam'iyyar APM ta amsa dukkan tambayoyin da waɗanda take tuhuma (INEC, APC, Tinubu, Kashim Shettima da Ibrahim Masari) suka gabatar game da ƙarar.

Kaɗan daga zaman Kotu ranar Litinin

A zaman farko da ya gudana ranar Litinin, 8 ga watan Mayu, 2023, Kotu ta kori ɗaya daga cikin kararrakin da aka shigar na kalubalantar nasarar zababben shugaban ƙasa.

Mai shari'a Tsammani ya kori karar jam'iyyar AA bayan lauyoyin jam'iyyar sun amince da janyewa bisa tanadin kundin dokokin zaɓe a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Da Obi: Abubuwa 5 Da Suka Wakana Yau A Kotun Sauraron Ƙarar Zaɓe

Haka zalika Kotu ta ɗage karar da Peter Obi ya shigar zuwa ranar Laraba 10 ga watan Mayu, 2023, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Tinubu Zai Sake Tafiya Zuwa Wata Kasar Waje? Hadiminsa Ya Bayyana Gaskiya

A wani labarin kuma zababben shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shirya tafiya zuwa kasar waje ana dab da rantsar da shi

Mai magana da yawun Tinubu, Mista Tunde Rahman, ya tabbatar da wannan ci gaban da cewa daga nan zuwa kowane lokacin Tinubu zai barin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel