Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa Ta Fara Zamanta: Kai Tsaye

Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa Ta Fara Zamanta: Kai Tsaye

A yau, Litinin, 8 ga watan Mayu ne, Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa za ta fara sauraron korafin kan sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Wannan zaman na da matukar muhimmanci domin shine daga karshe zai warware rikici kan sakamakon zaben shugaban kasar.

Kotun Zabe
Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa Za Ta Fara Zamanta. Hoto: KOLA SULAIMON/AFP, PATRICK MEINHARDT/AFP, PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

A kasance da Legit.ng Hausa domin samun rahotanni kan yadda zaman Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasar ke wakana.

Peter Obi ya fice daga Kotu

Ɗan takararar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar LP a zaben da aka kammala, Peter Obi, ya ja tawagarsa sun bar Kotun sauraron karar zaben shugaban kasa.

Peter Obi.
Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa Ta Fara Zamanta: Kai Tsaye
Asali: UGC

Kotun zabe ta ɗage karar Peter Obi da Labour Party

Ƙotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa mai zama a Abuja ta ɗage sauraron karar Labour Party da Peter Obi zuwa ranar 10 ga watan Mayu, 2023.

Jam'iyyar Labour Party da ɗan takararta na shugaban ƙasa sun kalubalanci nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kotu ta ɗage karar jam'iyyar APP

Kotun sauraron karar zaben shugaban ƙasa ta ɗage zama sauraron ƙorafin jam'iyyar APP zuwa ranar 10 ga watan Mayu, 2023, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

APP da ɗan takarart na shugaban ƙasa, Simon Nnadi, sun roki Kotu ta soke tikitin ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC bisa zarcin bai cancanta ya shiga zaɓe ba.

Sun kuma yi korafin cewa INEC ta basu kunya, ta ƙi bin tanadin kundin dokokin zaɓe 2022 wajen tura sakamakon zabe ta intanet, wanda a cewarsu hakan ne ya musu fashin nasara.

A yau Litinin, Lauyan APP, Obed Agu, ya bukaci APC da Tinubu su gaggauta aminta da shan kaye a zabe ba sai sun wahal da shari'a ba saboda kwararan hujjojin da APP ta mallaka.

A cewarsa, jam'iyyar APC na da hujjoji a gabanta wanda zasu gamsar da cewa ba Tinubu ne ya ci zaben shugaban ƙasa ba.

Amma lauyoyin APC da Tinubu, Lateef Fagbemi da Wole Olanipeku, sun shaida wa kotun cewa zasu maida martani kan wannan a lokacin da ya dace.

Ma'aikata sun koma tattaki a Abuja

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Ma'aikata da dama sun yi tattaki da kafarsu zuwa wurin aiki saboda jami'an tsaro sun toshe hanyar da Motoci zasu shiga cibiyar birnin Abuja.

Ma'aikata.
Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa Ta Fara Zamanta: Kai Tsaye Hoto: dailytrust
Asali: UGC

An samu cinkoson ababen hawa a Abuja

Motoci sun yi cirko-cirko yayin da jami'an tsaro suka toshe manyan titunan shiga cikin kwaryar birnin Abuja saboda zaman ƙotun sauraron ƙarar zabe, rahoton Daily Trust.

Cunkoson ababen hawa.
Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa Ta Fara Zamanta: Kai Tsaye Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Action Alliance ta janye ƙarar da ta shigar

Jam'iyyar Action Alliance ta janye korafin da ta shigar kan zaben shugaban ƙasan da aka kammala a Najeriya. Karanta cikakken labarin a nan.

Kotu zata saurari sauran korafi biyu ranar Talata

Mai shari'a Tsammani ya sanar da cewa Kotun ta tsara sauraron ragowar ƙararraki guda ɓiyu ranar Talata, 9 ga watan Mayu, 2023, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kararrakin da Kotu zata dawo ta saurara gobe Litinin su ne;

1. Ƙorafin Allied Peoples Movement (APM): CA/PEPC/04/2023

2. Korafin Atiku Abubakar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP): CA/PEPC/05/2023.

Korafi uku kaɗai Kotu zata saurara yau

Kwamitin Alƙalai da Mai shari'a Haruna Tsammani ke jagoranta ya sanar da cewa Kotu zata fara zamanta yau da sauraron korafe-korafe uku kacal.

Korafin sun kunshi:

1. Korafin jam'iyyar AA mai lamba CA/PEPC/01/2023

2. Ƙorafin jam'iyyar Action Peoples Party (APP): CA/PEPC/02/2023

3. Da korafin jam'iyyar Labour Party (LP): CA/PEPC/03/2023.

Lauyoyin Tinubu, Atiku da Peter Obi sun maida martani

Da suke martani daban-daban, lauyan zababben shugaban kasa, Wole Olanikpekun, Lauyan Atiku, Chris Uche da lauyan Peter Obi, Lizy Uzoukwu, sun tabbatarwa Kotu zasu bata haɗin kai da goyon baya.

Daga nan Alkalin ya karkare jawabinsa da cewa kowa zai gamsu da hukuncin da Kotu zata yanke bayan kammala sauraron ƙarar.

Kotu ta buɗe zaman shari'a

Kotu ta fara zaman sauraron shari'ar da misalin karfe 9:15 na safe, an fara da jawabin buɗewa daga bakin Alƙalin da zai jagoranci zaman, mai shari'a Haruna Tsammani, wanda zai shugabansu kwamitin alkalai 5.

Sauran alƙalan sun kunshi, Mai shari'a Stephen Adah, Mai shari'a Monsurat Bolaji-Yusuf, Mai shari'a Boloukuoromo Moses Ugo da kuma mai shari'a Abbah Mohammed.

Mai shari'a Tsammani ya tabbatar da cewa Alkalan ba zasu ɗauki wani bangare ba, zasu tsaya kan gaskiya kuma ya shawarci lauyoyin kowane ɓangare su guji kalamai nara daɗi.

Haka zalika ya buƙaci lauyoyin su ba da haɗin kai domin karƙare shari'a a cikin lokaci kuma su kaucewa gabatar da buƙatun da zasu ɓata lokacin Kotu.

Kotun sauraron karar zaben shugaban kasa: Abin da ake tsammanin zai garu a kotun zaben

A zaman sauraron jawabin sharar fage, wani babban lauya daga bangaren Tinubu ya fada wa The Punch abin da ake sa ran zai faru.

Lauyan da ya nemi a boye sunansa ya ce:

"Abin da za su yi kawai shine tsayar da ranar fara sauraron korafi, adadin shaidu, minti nawa ko wanne shaida zai yi, yadda za a karbi takardu; shine ake kira sharar fagen shari'a wato Pre-trial.
"Za su shirya jadawalin sauraron karar, adadin kwanakin da masu shigar da kara za su yi, adadin kwanakin da masu mayar da martani za su yi, yadda za mu karbi takardu, kwafin takardun na ainihi, za a karbe su a hakan ko kuma akwai rashin jituwa, yadda za a nuna rashin yarda da takardun?
"Kotun za ta yanke hukunci kan rashin karbar nan take ko kuma sai a cikin shari'ar? Wannan sune abin da za su faru gobe (Litinin)."

Kotun sauraron karar zaben shugaban kasa: Jerin yan takarar, jam'iyyu da ke son kotu ta kwace nasarar Tinubu

Yan takarar biyar ne ke kallubalantar nasarar Tinubu a zaben shugaban kasar na 2023.

1. Atiku Abubakar

2. Peter Obi

3. Action Peoples Party, (APP)

4. All Peoples Movement (APM)

5. Action Alliance (AA)

Matashiya: Yadda INEC ta ayyana Tinubu matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ayyana Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zabe bayan samun kuri'u 8,794,726.

A cewar hukumar, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya zo na biyu da kuri'u 6,984, 520, yayin da Peter Obi na Labour Party ya zo na uku da kuri'u 6,101,533.

Duba rahoton kai tsaye na sakamakon zaben na 2023 a nan.

Online view pixel