Yakubu Gowon Ya Roki Yan Najeriya Su Rungumi Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Zaben 2023

Yakubu Gowon Ya Roki Yan Najeriya Su Rungumi Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Zaben 2023

  • Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya roki yan Najeriya su aminta da duk hukuncin da Ƙotu ta yanke kan babban zaben 2023
  • Tsohon shugaban ƙasan ya ce ya kamata a bar Kotu ta gudanar da aikinta ba tare da tsoma baki ba
  • INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓe amma Atiku da Obi sun garzaya Kotu

Tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya roki yan Najeriya su rungumi duk hukuncin da Kotun sauraron ƙararrakin zabe ta yanke.

Channels tv ta tattato cewa Gawon ya faɗi haka ne a wurin taron da aka shirya domin girmama alƙalin Kotun koli, mai shari'a Chike Idigbe, ranar Alhamis.

Tsohon shugaban ƙasa, Yakubu Gowon.
Yakubu Gowon Ya Roki Yan Najeriya Su Rungumi Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Zaben 2023 Hoto: channelstv
Asali: UGC

Gowon ya roki ɗaukacin 'yan Najeriya su bar Kotu ta yi aikinta ba tare da katsa landan ba, domin bangaren shari'a na taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Faɗi Matsalar da Aka Samu Da halin da Ragowar 'Yan Najeriya Ke Ciki a Sudan

Wannan kira na tsohon shugaban ƙasa na zuwa ne bayan Kotun sauraron kararakin zaben shugaban ƙasa ta sanya ranar Litinin, 8 ga watan Mayu, 2023 domin fara zaman shari'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manyan mutanen da suka halarci wannan taro

Jiga-jigan da suka samu halartar taron da Gowon ya yi wannan kira sun ƙunshi tsohon shugaban Alƙalan Kotun koli, Mai shari'a Alfa Belgore da Ministan ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola.

Haka zalika karamin ministan kuɗi, kasafi da tsare-tsare ƙasa, Clem Agba, na cikin mahalarta taron da kuma wasu manyan lauyoyi (SAN), kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Idan baku manta ba, shugaban hukumar zaɓe (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Tinubu, ya zama zababben shugaban ƙasa bayan samun kuri'u mafiya rinjaye ya lallasa abokan karawarsa, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.

Kara karanta wannan

"Na Yi Nadamar Mulkin Buhari Saboda Manyan Abu 2 da Ya Kawo" Tsohon Makusancin Buhari Ya Tona Asiri

Bisa rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen, Atiku da Obi suka shigar da ƙara gaban Kotu, inda kowanensu ya nemi a soke zaben ko a ayyana shi a matsayin zababbe.

Aisha Buhari ta yaba wa mijinta kan ilimi

A wani labarin kuma Aisha Buhari Ta Magantu, Ta Jaddada Kudirin Mijinta Na Samar da Ilimi Mai Nagarta Ga Kowane Ɗan Najeriya

Uwar gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta ce a ko da yaushe mijinta a shirye yake ya inganta ɓangaren ilimin Najeriya.

Yayin da ya rage makonni mulkin Buhari ya ƙare, Aisha ta faɗi wasu kalamai masu jan hankali kan ilimin matasa a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel