Zabin Tinubu a Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Yi Kus-Kus da Shugaba Buhari, Bayanai Sun Bayyana

Zabin Tinubu a Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Yi Kus-Kus da Shugaba Buhari, Bayanai Sun Bayyana

  • Zaɓaɓɓen sanatan Ikot-Ekpene a majalisar dattawa ya gana da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a fadar sa
  • Sanata Godswill Akpabio ya gana da shugaba Buhari ne domin sanar masa da aniyar sa ta zama shugaban majalisar dattawa ta 10
  • Akpabio ya bayyana abubuwan cigaba da zai kawo idan ya samu ɗarewa kan shugabancin majalisar

Abuja - Tsohon ministan yankin Niger Delta kuma zaɓaɓɓen sanata a yanzu, a mazaɓar sanatan Ikot-Ekpene, Godswill Akpabio, ya gayawa shugaba Buhari niyyar sa ta zama shugaban majalisar dattawa ta 10.

Ya bayyana hakan ne da yammacin ranar Lahadi, bayan ya sanya labule da shugaba Buhari a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, cewar rahoton Daily Trust.

Akpabio ya gayawa shugaba Buhari aniyar sa ta son zama shugaban majalisa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sanata Godswill Akpabio a Aso Villa Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Vanguard ta rahoto cewa, Akpabio ya ce a matsayin shugaban majalisar dattawa, zai yi aiki hannu da hannu da gwamnatin Asiwaju Bola Tinubu, domin samar wa ƴan Najeriya abubuwan yi, musamman matasa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yari Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Arewa Ta Cancanci Shugabancin Majalisar Dattawa

Zaɓaɓɓen sanatan ya godewa shugaba Buhari, bisa damar da ya ba shi, ta yin aiki a matsayin minista a gwamnatin sa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka tambaye shi ko wane irin shiri ya ke da shi kan ƴan Najeriya idan ya zama shugaban majalisar, tsohon ministan sai ya kada baki ya ce:

"Akpabio sananne a matsayin mai kawo sauyi. Akpabio sananne ne a matsayin mutum mai aiki da cikawa. Idan ba ku manta ba lokacin ina gwamna na kawo cigaba sosai a fannin ababen more rayuwa, ilmi, jindaɗin jama'a da kuma samar da ayyukan yi."
"Ina da niyyar kawo sauye-sauye da dama a majalisa, kan yadda ake gudanar da ita domin taimakawa gwamnati mai kamawa ta yi nasara. Za mu yi komai kan yadda ya dace, za mu kawo mutunta kunɗin tsarin mulki da mutunta ƴan Najeriya."

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ja Hankalin Atiku da Obi, Ya Faɗi Abinda Ya Rage Musu Kan Zaben 2023

"Za mu magance matsaloli ta hanyar dokokin da za su samar wa da ƴan Najeriya ayyukan yi musamman matasa. Zaman ɗar-ɗar da ake yi a ƙasa, za mu yi bakin ƙoƙarin mu wajen samar da dokoki masu kyau sannan da taimakawa gwamnati samar da tsare-tsaren da za su samar wa da matasa abin yi."

Dan Takarar Gwamnan APC a Bauchi Ya Garzaya Kotu

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Bauchi, ya nuna fatan kwato nasarar sa a kotu.

Abubakar Baba Saddique, wanda ya sha kashi a hannun gwamna Bala Mohammed na PDP, ya ce yana sa ran kotun za ta dawo masa da nasarar sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel