Zababben Shugaban Kasa Tinubu Ya Karbi Bakuncin Wike Da Makinde a Abuja

Zababben Shugaban Kasa Tinubu Ya Karbi Bakuncin Wike Da Makinde a Abuja

  • Gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) biyu sun ziyarci zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • A cewar rahotanni, gwamnonin biyu sune Gwamnan Ribas Nyesom Wike da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo
  • An karbi bakuncin yan siyasan biyu ne a ranar Juma'a, 28 ga watan Afrilu, a gidan gwamnati na 'Defence House' da ke Abuja, inda Tinubu yake da zama

Abuja - Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya karbi bakuncin gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a gidan gwamnati na 'Defence House', Abuja a ranar Juma'a.

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, sun yi wata ganawa da shugaban kasa mai jiran gado.

Manyan yan siyasar Najeriya
Zababben Shugaban Kasa Tinubu Ya Karbi Bakuncin Wike Da Makinde a Abuja Hoto: @DOlusegun, @kc_journalist
Asali: Twitter

Gwmanonin biyu suna daga cikin fusatattun gwamnonin G-5 na PDP da suka ki yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kuma dan takarar PDP a zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabrairu aiki.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP 2 Sun Gana da Tinubu a Abuja, Gwamna Wike Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

Sun dage cewa sai shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, ya yi murabus gabannin babban zaben kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya a sansanin Tinubu ta tabbatar wa Daily Trust a ranar Juma'a, 28 ga watan Afrilu cewa gwamnonin biyu sun gana da Tinubu a Abuja, amma sun dage cewa taron bai da nasaba da siyasa.

Ya ce:

"Gwamna Seyi Makinde, zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike sun gana a Abuja a yau.
"Sun ce sun je kai ziyarar bangirma ne ga zababben shugaban kasa; cewa zabe ya wuce kuma yanzu lokaci ne na fuskantar gwamnati, kuma za su marawa Tinubu baya da hadin kai don ya yi nasara da juya arzikin kasar."

Da wasu manema labarai suka nemi jin karin bayani, ya ce:

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Zababben Shugaban Kasa Tinubu, Hotuna Sun Bayyana

"Ziyararsu bai da alaka da jam'iyya, ziyarar fatan alkhairi ne."

MURIC ta nemi a hukumomin tsaro su bai wa Bola Tinubu kariya

A wani labarin, kungiyar MURIC ta bukaci hukumomin tsaro da su kara ba wa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima kariya gabannin bikin rantsarwa.

A cewar kungiyar kare hakkin Musulmin, wannan kiran ya zama saboda irin kalaman da ke fitowa daga bangaren abokan hamayya a siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel