Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu

Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a Aso Villa
  • Shugaba mai barin gado tare da mai jiran gado sun yi Sallar Jummu'a tare a Masallacin fadar shugaban ƙasa, Abuja
  • Wannan na zuwa ne awanni 34 bayan Buhari ya ce jam'iyyun adawa sun sha kaye ne saboda ci da zuci

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya karɓi bakuncin zababben shugaban kasa, Alhaji Ahmed Bola Tinubu, a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Shugabannin biyu, shugaba mai barin gado da kuma shugaban ƙasa mai jiran gado sun yi Sallar Jummu'a tare a Masallacin fadar fadar shugaban ƙasa yau Jumu'a 28 ga watan Afrilu, 2023.

Buhari da Tinubu.
Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu Hotuna: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Channels tv ta tattaro cewa bayan kammala Sallah ne, Tinubu ya kama hanya ya bar cikin Aso Villa ba tare da ya yi jawabi ga manema labarai ba.

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: Zababɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, Ya Gana da Wasu Gwamnoni da Sarkin Kano

Kafin nan, shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi tare da ɗan takarar gwamna a inuwar APC a zaben 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan ziyara dai na zuwa ne awanni 24 bayan Buhari ya yi ikirarin cewa jam'iyyun adawa sun sha kashi a zaben shugaban kasan da aka kammala sakamakon ci da zuci.

Ya ce a ɗaya bangaren kuma jam'iyyar APC mai mulki ta yi aiki tukuru don samun nasara inda ya ce, "Mun yi aiki tuƙuru kuma mun basu kunya."

Yayin da ya karɓi bakuncin gwamnonin APC karkashin jagorancin gwamna Atiku Bagudu, shugaba Buhari ya ce:

"Sun tafi suna faɗawa masu goyon bayansu na kasashen duniya cewa babu makawa sai sun kawar da jam'iyyar APC. Ga shi yanzu ci da zucinsu ya haifar musu da matsaloli."

Kara karanta wannan

"Ba Zan Daɗe a Daura Ba" Shugaba Buhari Ya Canja Garin da Zai Koma Bayan Miƙa Mulki Ga Tinubu

"A yanzu sun rasa yadda zasu yi su gamsar da yan kasahen wajen da suka goya musu ba ya, ta ya suka gaza kayar da mu."

Tinubu: An Bukaci Hukumomin Tsaro Su Kara Ba Zababben Shugaban Kasa Kariya

A wani labarin kuma An Bukaci Hukumomin Tsaro Su Kare Rayuwar Zababben Shugaban Kasa

Ƙungiyar kare haƙƙin musulmai a Najeriya MURIC ta nemi DSS da sauran hukumomin tsaro a Najeriya da su kara matsa kaimi wajen ba da kariya ga Tinubu da Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262