Wani babban jigon APC a jihar Zamfara ya koma jam'iyyar PDP, ya shiga tseren takara a 2023

Wani babban jigon APC a jihar Zamfara ya koma jam'iyyar PDP, ya shiga tseren takara a 2023

  • Yayin da jam'iyyar APC ke ganin ta fara gano bakin zaren rikicinta, wani jigo ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP mai adawa
  • Tsohon babban daraktan First Bank PLc, Dakta Dauda Lawal, bayan komawa PDP ya ayyana kudirin tsayawa takara a zaɓen 2023
  • Ya ce a matsayinsa na ɗan jiha mai kishi ya zama wajibi ya fito ya ba da gudummuwa don ceto jihar daga halin rashin tsaro

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Wani jigon APC a jihar Zamfara, Ɗakta Dauda Lawal, ya fice daga jam'iyya mai mulki ya koma PDP, kamar yadda Chennels tv ta ruwaito.

Lawal, tsohon babban daraktan First Bank, ya kuma ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Zamfara ƙarƙashin inuwar sabuwar jam'iyyarsa PDP.

Ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi gaban dandazon masoya da magoya bayansa a gidansa da ke Gusau, babban birnin Zamfara.

Kara karanta wannan

Bayan kokarin sulhu, Gwamna ya shata layin yaƙi da yan bindiga, ya ce zai hana su sakat

Taswirar jihar Zamfara.
Wani babban jigon APC a jihar Zamfara ya koma jam'iyyar PDP, ya shiga tseren takara a 2023 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ɗan takarar gwamnan ya bayyana gwamnatin APC a matakin ƙasa da jiha da matsayin wacce ta gaza, inda ya ƙara da cewa jam'iyyar ta gaji kuma ta yi rauni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ya tsaya takara a PDP?

Dakta Lawal ya yi bayanin cewa ya yanke shawarar shiga tseren takarar gwamna ne saboda damuwarsa da tsaro da kuma kalubalen tattalin arziƙi da ya addabi Zamfara.

Ya ce jahar Zamfara ce kan gaba da matsalar tsaro ta fi yi wa katutu, bisa haka a matsayin ɗan jiha mai kishi akwai bukatar ya ba da gudummuwa wajen kawo canji a harkokin gwamnati.

A kalamansa ya ce:

"Kowanen mu ya na da masaniyar halin tsaron da muka fuskanta, a yau zan iya cewa jahar Zamfara na ɗaya daga cikin wurin da lamarin ya fi muni idan ma ba za'a iya cewa ita ce lamba ɗaya ba."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ga Najeriya: Ba zan huta ba har sai an samu zaman lafiya a kasar nan

"Kuma maganar gaskiya idan ba bu tsaro, rayuwa ba zata yi dadi da amfani ba kuma ba yadda muka iya."

A wani labarin kuma Tsohon ɗan majalisa ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, Ya lale kuɗi ya sayi Fom

Tsohon ɗan majalisar tarayya , Dakta Usman Bugaje, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da ke tafe.

Tsohon hadimin Atiku Abubakar ɗin ya ce Najeriya ta tsaya cak tana bukatar jajirtattun shugabanni a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel