Gaskiyar Magana Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya APC Ta Kasa Karbar Mulki a Hannun PDP a Wata Babbar Jiha
- Gaskiya ta fito fili dangane da dalilin da ya sanya jam'iyyar APC ta kasa samun nasara a zaɓen gwamnan jihar Oyo
- Wata ƙungiyar ƴaƴan jam'iyyar ta ce faɗa da juna da ƴaƴan jam'iyyar ke yi a jihar shi ya ba su cikas
- Ƙungiyar ta kuma yi kira da ƴaƴan jam'iyyar APC a jihar da su kai zuciya nesa su dawo a samu sasanci
Jihar Oyo - Wasu magoya bayan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, a jihar Oyo sun bayyana cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta sha kashi a zaɓen gwamnan jihar ne saboda rikicin cikin gida da ta ke fama da shi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, magoya bayan waɗanɗa suke a ƙarƙashin ƙungiyar Disciples of Justice (DOJ), sun ce halayyar ɗan takarar gwamnan APC na jihar, Sanata Teslim Folarin, babban koma baya ce.
Jagoran ƙungiyar na ƙasa, Hakeem Alawuje, a wani taro da manema labarai a birnin Legas, ya ce ɗan takarar gwamnan ya yi watsi da mafi yawan ƴaƴan jam'iyyar inda ya janyo tsaffin ƴaƴan jam'iyyar PDP suka kankane komai.
Ya ce ɗan takarar gwamnan na APC ya kwace damar sa, sannan ba daidai bane ya fara neman a bashi muƙamin minista.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai, ya kuma kira ga dukkanin ƴaƴan jam'iyyar da aka ɓata wa rai suka fice daga jam'iyyar da su dawo cikin ta domin babu inda ya kai gida daɗi, cewar rahoton Vanguard
“Yakamata mu fara shirin sasantawa da kowa cikin gaggawa, da yadda zamu samu fahimtar juna wanda zai amfani jam'iyyar, ƴaƴan ta da kuma mutanen jihar Oyo." A cewarsa
Bangaren Folarin ya yi martani
Da aka nemi jin ta bakin kakakin ɗan takarar gwamnan, Yekini Olaniyi, ya musanta zarge-zargen da ake yi wa ubangidan sa inda ya kira ƴan ƙungiyar da masu ɗaukar nauyin su a matsayin sakarkaru.
Ya ce wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC ta jihar Oyo an dama da su wanda hakan ne ya sanya jam'iyyar ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa a jihar.
Dangane da zaɓen gwamnan jihar kuma ya ce APC ba ta yi rashin nasara ba a hannun Makinde, amma ƴaƴan jam'iyyar ne suka ci dunduniyar Folarin.
Ya kuma ƙalubalanci ƙungiyar da ta kawo hujjar cewa Folarin yana zawarcin a ba shi muƙamin minista a gwamnatin Tinubu.
Sanatan APC Ya Kawo Hujjoji, Ya Fadi Yankin da Ya Dace Sabon Shugaban Majalisa Ya Fito
A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda sanatan APC ya kawo hujjojin da yakamata ace sabon shugaban majalisa ya fito daga wani yanki a ƙasar nan.
Sanata Osita Izunaso ya ƙara jaddada cewa har yanzu fa shugabancin majalisar dattawa, da shi ya fi dacewa.
Asali: Legit.ng