Matasan Jam'iyyar APC Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Ondo

Matasan Jam'iyyar APC Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Ondo

  • Abubuwa sun kara dagulewa jam'iyyar PDP tun bayan shan kashi a babban zaɓen shugaban kasa da ya gabata
  • Wasu gungun matasa sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a karamar hukumar Akure ta kudu, jihar Ondo
  • Sun ce ganin yadda APC ke taimaka wa matasa suna rayuwa mai kyau, ba zasu bari a barsu a baya ba

Ondo - Wasu Matasa da aka san 'yan gani kashenin mambobin Peoples Democratic Party (PDP) ne a ƙaramar hukumar Akure ta kudu, jihar Ondo sun koma All Progressives Congress (APC) ranar Talata.

Leadership ta ce Matasan, shugabannin ƙungiyar matasan PDP sun ɗauki wannan matakin ne bayan hango wurin zama a APC ganin yadda take kula da mambobi musamman matasa.

Sauya sheƙa a Najeriya.
Matasan Jam'iyyar APC Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Ondo Hoto: leadership
Asali: UGC

Da yake maraba da tsoffin mambobin PDP zuwa inuwar am'iyyarsu, shugaban APC na Ondo, Ade Adetimehin, ya tabbatar musu da cewa gida suka zo ba za'a nuna musu banbanci ba.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha

Meyasa matasa suka yanke shawarin shiga APC?

Jagoran masu sauya sheƙar, Seriki Katike, ya ce matasan sun yanke shawarin rungumar APC ne saboda ganin yadda matasa maza da mata, waɗanda aka ba tallafi suka fara kasuwanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa ya ce:

"Sun ga wasu daga cikin matasan waɗanda mambobin APC ne a maƙotanmu, an nuna musu a zahiranci jam'iyya na sane da su kuma tana girmama walwalar mambobinta."

Seriki Katike, wanda makanike ne mai gyaran ababen hawa, ya ja hankalin matasan zuwa APC, ya ce shi kaɗai ya san yadda shagonsa yake gabanin ya rungumi APC.

A cewarsa, a baya da karfin tuwo yake ayyukansa, amna yanzun ya samu kayan aikin da suka sauƙaƙa masa ayyukansa tun da ya bar jam'iyyar PDP.

Independent ta rahoto shi yana cewa:

"Shiyasa kuka ganmu a nan, muna son rayuwar matasa ta sauya ta zama mai tasiri kuma shugaban APC na jiha, Ade Adetimehin, ya tabbatar mana da zamu samu goyon baya."

Kara karanta wannan

Rikici Ya Dawo Ɗanye, APC Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Da Wani Babban Jigo

Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban LP da Wasu Jiga-Jigai Uku

A wani labarin kuma Babbar Kotu a Abuja ya dakatar da shugaban LP, Sakatare da wasu shugabanni 2 daga bayyana kansu a matsayin shugabanni

Hakan ya biyo karar da aka shigar gaban Alkalin Kotun kan tuhumar mutanen huɗu da aikata muggan laifuka a babban zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel