"Bamu Da Hannu a Shirin Kifar Da Gwamnati", Jam'iyyar Labour Party

"Bamu Da Hannu a Shirin Kifar Da Gwamnati", Jam'iyyar Labour Party

  • Jam'iyyar Labour Party ta fito fili ta bayyana cewa ba ta da hannu a cikin shirin kifar da gwamnati a ƙasar nan
  • Jam'iyyar ta bayyana hakan ne ta hannun kakakin ta, Yunusa Tanko, wanda yace jam'iyyar su mai bin doka ce da oda
  • Hukumar DSS dai ta bankaɗo shirin da ake ƙullawa na kifar da gwamnati a ƙasar nan domin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya

Jihar Legas: Jam'iyyar Labour Party (LP) ta bayyana cewa ba ta da hannu a cikin kowane irin shirin kifar da gwamnati. Jam'iyyar ta bayyana hakan ne ta hannun kakakin ta, Yunusa Tanko, a ranar Alhamis. Rahoton Channels Tv

A ranar Laraba, hukumar ƴan sandan farin kaya ta Najeriya (DSS), ta bankaɗo wani shirin kitimurmurar da ake ƙullawa domin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.

Kara karanta wannan

Malamin Addinin Musulunci Ya Dau Zafi Ya Bayyana Illar Makarkashiyar Hana Rantsar Da Tinubu

Labour
"Bamu Da Hannu a Shirin Kifar Da Gwamnati", Jam'iyyar Labour Party Hoto: Arise News
Asali: UGC

Kakakin hukumar, Peter Afunanya, shine ya bayyana hakan inda ya bayyana cewa hukumar ta gano wasu masu hannu a cikin shirin da ake ƙullawa. Rahoton Vanguard

Da yake magana kan lamarin a shirin gidan talabijin na Channels tv mai suna 'Lunch time politics', kakakin jam'iyyar Labour Party, ya bayyana cewa jam'iyyar bata kitsa wani shirin kifar da gwamnati, inda ya bayyana hakan a matsayin cin amanar ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bamu da hannu a kowane irin shirin kifar da gwamnati" Inji shi
"Amma abinda nake cewa shine zamu kare martabar ƴan Najeriya bisa tsarin doka wanda yayi tanadin cewa idan an ɓata maka rai, kana da damar yin zanga-zanga, kuma zaka yi ta ne tare da samun kariya daga jami'an tsaro."
"Abinda zamu yi kenan, amma ba zamu goyi bayan kifar da gwamnati ba ta kowace hanya."

Kakakin ya kuma zargi hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro na ƙin kare abinda ƴan Najeriya suke so a lokacin babban zaɓen 2023, inda yayi iƙirarin cewa wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar su an hana su yin zaɓe a wasu sassan ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Babban Abinda Ya Sa Abba Gida-Gida Ya Lallasa APC a Zaben Gwamna a Kano

"DSS da sauran hukumomin tsaro su fito su kare mu ko da kuwa muna akan tituna muna zanga-zanga."

A cewar sa, jam'iyyar LP ba zata yi wani abu ba da ya saɓawa doka sannan zata bi hanyar da ta dace wajen neman haƙƙin ta da aka tauye.

Ku Kwamushe Masu Yunkurin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi”: IPAC Ga DSS

A wani labarin na daban kuma, ƙungiyar IPAC tayi kira ga hukumar DSS da tayi ram da masu yunƙurin kafa gwamnatin wucin gadi a ƙasar nan.

Shugaban ƙuniyar, Sani Yabagi shine yayi wannan kiran ga hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng