Gwamnan APC Ya Samu Hujjojin Yadda Aka Yi Amfani da Sojoji Wajen Hana Shi Zarcewa

Gwamnan APC Ya Samu Hujjojin Yadda Aka Yi Amfani da Sojoji Wajen Hana Shi Zarcewa

  • Muhammad Bello Matawalle ya tuhumi sojoji da taimakawa wajen rashin nasarar APC a Zamfara
  • Gwamnan ya ce a duk rumfar zabe sai da aka baza soja akalla 50 domin a kai jam’iyyar APC kasa
  • Lawal Dauda Dare ya doke Bello Matawalle, ya hana Gwamnan samun tazarce duk da karfin APC

Zamfara - Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara yana ganin ba zaben gaskiya aka yi a 2023 ba, hakan ya jawo ya rasa kujerarsa.

A wata zantawa da aka yi da shi a DW Hausa, Muhammad Bello Matawalle ya yi zargin cewa an yi amfani da jami’an tsaro wajen tafka magudi.

Mai girma Gwamnan yake cewa su na da hujjojin da ke nuna sojoji sun rika muzgunawa magoya bayansu masu niyyar kada kuri’a ga APC.

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

An ji Bello Matawalle yana kokawa cewa a maimakon ayi amfani da sojoji wajen kawo karshen rashin tsaro, sai aka yi amfani da su a harkar zabe.

Sojoji 50 a duk rumfar zabe

Gwamnan mai shirin barin-gado ya ce ta kai ana baza sojoji 50 a rumfar zabe saboda a shirya murdiya, kamar yadda ya fada, akwai hujjoji a bidiyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Gwamna Matawalle motoci fiye da 300 suka shiga jihar Zamfara a lokacin da ake shirin zabe, ya ce sojojin sun isa su gama da 'yan bindiga.

Kamfen APC
Kamfen APC a Zamfara Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Kuma duk wata rumfa ta Zamfara ta zabe, babu wanda ke da soja kasa da 50 ga rumfunan zaben Zamfara.
Sannan kuma kai tsaye za ka ga cewa kiri-kiri idan ‘dan APC ka ke, ka ga soja yana bugunka cewa ba ka zabe.

- Muhammad Bello Matawalle

Kara karanta wannan

Dani za a yi: Tsohon gwamnan jihar Arewa ya shiga jerin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa

Matawalle zai je kotun zabe?

Da DW Hausa ta tambaye shi ko zai shigar da kara a kotu, Gwamnan ya nuna matakin ya rage ga jam’iyya, ya ce bai isa ya hana APC zuwa kotu ba.

Tun farko Mai girma Gwamna ya ce a matsayinsa na Musulmi yana mai godiya ga Allah SWT domin babu wanda ya yi tunanin zai samu mulki a 2019.

A zaben 2023, Lawal Dauda Dare da ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP ne ya yi galaba a kan Bello Matawalle, ya hana shi zarcewa a kan mulki.

Siyasar Kano sai Kano

A yau aka ji labari Abba Kabir Yusuf ya nemi Nasiru Gawuna ya rungumi kaddara, ya yi koyi da abin da Rabiu Kwankwaso ya yi bayan rasa takarar 2003.

Ganin an ji ‘dan takaran ya ce ko bai yi nasara ba, zai karbi zabin da Allah (SWT) ya yi, zababben Gwamnan ya nemi Gawuna ya cika alkawarin na sa.

Kara karanta wannan

Mansur Sokoto Ya Yi Wa Dauda Lawal Nasihar Ratsa Zuciya Bayan Cin Zaben Gwamna

Asali: Legit.ng

Online view pixel