Abba Gida Gida Ya Bi Tafarkin Kwankwaso, Ya ce Babu Ruwan Iyalinsa da Gwamnatinsu

Abba Gida Gida Ya Bi Tafarkin Kwankwaso, Ya ce Babu Ruwan Iyalinsa da Gwamnatinsu

  • Abba Kabir Yusuf ya yi jawabi bayan ya karbi takardar shaidar lashe zaben Gwamnan Kano
  • Zababben Gwamnan jihar Kano a NNPP ya ce iyalinsa ba za su shiga harkar shugabanci ba
  • Abba Gida Gida yana so Nasiru Yusuf Gawuna ya dauki zaben 2023 a matsayin kaddarar Allah

Kano - Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa a gwamnatinsa, ba za a rika damawa da matansa da iyalinsa har ta kai su na da rawar da za su taka ba.

Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida, ya bayyana haka yayin da yake jawabi wajen karbar takardar shaidar lashe zaben Gwamna.

Daily Trust ta ce watakila hakan bai rasa nasaba da zargin da ake yi wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cusa uwargidarsa a wajen harkar mulki.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Zama Dole Tinubu Ya Fara Yi Da Zarar An Rantsar Da Shi, Festus Keyamo Ya Bayyana

Zababben Gwamnan ya ce a gwamnatinsa, iyali da dangi ba su da ta-cewa domin kuwa ba tare da su zai yi rantsuwar zama Gwamnan jihar Kano ba.

Mata na ba za su kasance cikin gwamnati ba. ‘Ya ‘ya na ba su cikin shugabancin jama’a. Kuma zan iya cewa haka abin yake game da mataimaki na.

- Abba Kabir Yusuf

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abba Gida Gida ya ce a zaben da aka yi a watan na Maris, babu wanda ya yi nasara ko ya ji kunya, yana mai kira ga Nasir Yusuf Gawuna da ya sallama.

Abba Gida Gida
Abba Kabir Yusuf ya karbi satifiket Hoto: @salisuyahayahototo
Asali: Facebook

Kira ga 'Dan takaran APC

An rahoto Abba yana cewa ya ji Nasir Yusuf Gawuna a lokacin kamfe yana cewa zai amince da zabin Ubangiji, ya ce ya kamata ya nuna hakan a aikace.

Mun ji Nasir Gawuna yana fadawa manema labarai kafin a fadi sakamako cewa idan bai yi nasara ba, zai karbi zabin da Ubangiji ya yi.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Aike da Babban Saƙo Ga Tinubu, Ya Faɗi Faɗi Abinda Ya Kamata Ya Yi Wa Wike

Saboda haka mu na kira gare shi ya fito ya yi wa mutane jawabi, ya tabbatar da ya rungumi wannan a matsayin zabin Ubangijin SWT.

- Abba Kabir Yusuf

Gwamnan mai jiran gado ya bukaci Gawuwa da ya yi takara a APC da ya yi koyi da Rabiu Kwankwaso wanda ya hakura da ya rasa takara a 2003.

Abba Kabir Yusuf wanda ya lashe zaben Gwamna a jam’iyyar NNPP ya yabi aikin da jami’an tsaro suka yi a zaben bana, amma ya ce akwai gyara.

‘Dan siyasar ya gargadi jami’an tsaron da suka goyi bayan bangaren gwamnati da jam’iyya mai-ci, yake cewa ya kamata su guji sa siyasa a aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel