Bola Tinubu Ya Soke Bikin Cika Shekara 71, Ya Komawa Allah Gadan-Gadan a Bana

Bola Tinubu Ya Soke Bikin Cika Shekara 71, Ya Komawa Allah Gadan-Gadan a Bana

  • Babu wani bikin da za a shirya a shekarar bana domin taya Asiwaju Bola Tinubu cika shekara 71
  • A rana irin ta yau ake murnar zagayowar ranar haihuwar ‘dan siyasar da zai karbi mulkin Najeriya
  • Yayin da ranar ta fado a lokacin azumi, Bola Tinubu ya zabi a shirya zaman addu’o’i a masallatai

Abuja - A maimakon ayi biki yadda aka saba domin taya shi murnar kara shekara a ban-kasa, wannan karo Asiwaju Bola Tinubu ya canza tsari.

Jaridar Premium Times ta ce Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zabi a shirya addu’o’i na musamman a yau Laraba da yake cika shekara 71 da haihuwa.

Za ayi wadannan taron addu’o’i ne a Legas da wasu bangarorin kasar nan kamar yadda jawabin da Hadimin ‘dan siyasar, Tunde Rahman ya nuna.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta Kunshe Biliyoyin Kudi Wajen Saida Fam Ga Masu Sha’awar Takara

A jawabinsa da ya fitar a farkon makon da ake ciki, Rahman ya ce a Legas za ayi addu’o’i a wurare biyar, daga ciki akwai babban masallaci na jihar.

Addu'o'i a masallatai

Rahoton ya ce baya ga haka, za ayi irin wadannan taro a manyan masallatan da ke Alausa da Ikeja domin a roko Ubangiji SWT cigaba da zaman lafiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za a hada da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mai dakinsa, Aisha Muhammadu Buhari, Bola Tinubu da matarsa, Oluremi Tinubu a rokon.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a masallaci Hoto: nationaldailyng.com
Asali: UGC

Sauran wadanda za a hada a addu’o’in da za ayi sun kunshi Kashim Shettima da uwargidarsa, Gwamnan Legas da kuma sauran ‘yan majalisun jihar.

Karatu, huduba da addu'o'i

Sanarwar ta nuna cewa Limamin nan, Akeem Kosoko zai jagoranci taron addu’ar da za ayi a babban masallacin da yake Alausa da karfe 10:00 na safiya.

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

Baya ga karatu, Imam Akeem Kosoko zai hada da huduba da kuma karatun Al-Kur’ani mai tsarki.

Shekaru 3 ba ayi biki ba

The Cable ta ce shekaru uku kenan Bola Tinubu ya na fasa yin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa, a 2022 an yi haka ne saboda rashin tsaro.

A daidai irin wannan lokaci aka yi garkuwa da mutane a jirgin kasan Abuja-Kaduna, a shekarar 2020 kuwa ana tsakiyar annobar cutar nan ta COVID-19.

Fasto zai zama Gwamna

Bayan kusan tsawon shekaru biyar, kun samu labari mulkin jihar Benuwai ya sake dawowa hannun Jam'iyyar APC ta hannun Rabaren Hyacinth Alia.

APC ta samu kuri’u 473, 933, ta bar ‘Dan takaran PDP da 223, 913 a zaben Gwamna na 2023. Ana tunanin karfin coci ya taimaka wajen rashin nasarar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel