Duk da Guguwar Peter Obi, Jam’iyyar LP Ta Gaza Samun Gwamna ko 1 a Zaben Jihohi

Duk da Guguwar Peter Obi, Jam’iyyar LP Ta Gaza Samun Gwamna ko 1 a Zaben Jihohi

  • Har yanzu babu wata Jihar Najeriya da LP ta samu nasara a zaben Gwamnonin jihohi da aka yi
  • Jam’iyyar LP ta zo ta uku da kuri’u miliyan 6 a zaben shugaban kasa, yanzu lamarin ya canza
  • ‘Yan takaran Gwamnonin da LP ta tsaida ba su yi irin kokarin da Peter Obi ya yi a Fubrairu ba

Abuja - Kusan abin da magoya bayan Peter Obi da ake kira ‘Obidients’su ka yi tunani ba shi ya faru a zaben Gwamnonin jihohi da aka shirya ba.

A wani rahoto da Vanguard ta fitar, an ji yadda Jam’iyyar Labour Party ta gagara yin nasara a ko da Jiha guda ganin kokarinta a zaben shugaban kasa.

Har a yankin Kudu maso gabas da jam’iyyar hamayyar da ‘dan takaranta a 2023 watau Peter Obi suka doke APC da PDP, ba su tabuka abin a yaba ba.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Jihohin da Ba'a Kammala Zaben Gwamna Ba da Waɗanda INEC Ta Dakatar da Tattara Sakamako

Idan aka yi la’akari da sakamakon INEC, har zuwa yanzu, babu LP a jerin jam’iyyun da suka lashe zaben Gwamna ko akalla su ke rike da mulkin jihar.

An san sakamakon Jihohi 24

Hukumar zabe na kasa ta sanar da sakamakon Jihohi 24 a cikin 28 da aka yi takara. Jam’iyyar APC na da jihohi 15, PDP ta samu 8, NNPP kuwa daya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jam’iyyar NNPP wanda ta zo na hudu a zaben shugaban kasa ta iya samun mulki a jihar Kano, mahaifar ‘dan takaranta, Rabiu Musa Kwankwaso.

Peter Obi
Peter Obi da Yusuf Datti Ahmed Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Amma ‘Yan Obidients za su sa rai abubuwa su canza musamman ganin akwai jihohi biyu (watau Adamawa da Kebbi) da ba a kammala zaben ba tukuna.

Akwai rai a Abia da Enugu

Rahoton ya ce LP ta na burin kai labari a Abia da Enugu inda aka dakatar da tattara kuri’u, musamman ganin jihohin su na inda jam’iyyar ke da karfi.

An fi yi wa jam’iyyar ta su Peter Obi hangen nasara a wadannan jihohi biyu domin ana ganin ‘dan takararta ko na PDP zai zama sabon Gwamna a Mayu.

Kara karanta wannan

Wasu ‘Yan Takaran APC Za Su Kotu Domin Karbe Nasarar PDP a Zaben Gwamnoni

A jihohin Arewa da Obi ya samu kuri’u masu yawa a zaben shugaban kasa na watan Fubrairu, LP ba ta iya kamanta nasararta a takarar Gwamnoni ba.

A zaben na ranar Asabar, APC da PDP ne suka yi galaba a Filato da Nasarawa. Ba a batun LP a Kuros Riba, Delta, Ebonyi sai a Legas ne ta zo ta biyu.

Fayose da Tambuwal

An samu labari cewa Ayo Fayose ya yi matukar murna da faduwar ‘dan takaran Aminu Tambuwal a zaben sabon Gwamnan jihar Sokoto na 2023.

Fayose yake cewa Aminu Tambuwal ya ci amanar PDP da Asiwaju Tinubu, sannan ya ci amanar Nyesom Wike da ya mara masa baya a zaben 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng