Zaben Gwamnan Kano: Za Mu Kwamushe Duk Wanda Ya Dauki Makami a Ranar Asabar – Yan Sanda

Zaben Gwamnan Kano: Za Mu Kwamushe Duk Wanda Ya Dauki Makami a Ranar Asabar – Yan Sanda

  • Kasa da sa'o'i 48 kafin zaben gwamna, rundunar yan sanda ta yi gargadi ga al'ummar jihar Kano
  • Rundunar yan sanda ta bakin DIG Hafiz Muhammad Inuwa ta sha alwashin daukar mummunan mataki kan duk wanda ya dauki makami a ranar zabe
  • Yan sandan sun gargadi yan siyasa da mabiyansu a kan su guji aikata abun da zai ta da tarzoma yayin zaben

Kano - Gabannin zaben gwamnoni na ranar Asabar, 18 ga watan Maris, rundunar yan sandan Najeriya ta yi gagarumin gargadi ga yan siyasa da magoya bayansu a kan zaben.

DIG Hafiz Muhammad Inuwa wanda ke dauke da alhakin kula da harkokin zaben 2023 a yankin arewa maso yamma ya bukaci yan siyasa da mabiyansu da su kaurawa aikata duk wani abu da ka iya tayar da hankulan masu zabe.

Kara karanta wannan

Zabo Tinubu ya ba mutane da yawa mamaki, Garba Shehu ya yi magana mai daukar hankali

Ya kuma bayyana cewa Sufeto janar na yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya bukace su da su ja hankalin yan siyasa da masu fada aji a kan su gargadi mabiyansu gabannin zaben, rahoton Aminiya.

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
Zaben Gwamnan Kano: Za Mu Kwamushe Duk Wanda Ya Dauki Makami a Ranar Asabar – Yan Sanda Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne a Jihar Kano, a ci gaba da shirye-shirye da rundunar ke yi na tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin Sufeto Janar na yan sandan ya bayyana hakan ne a Kano, yayin da rundunar ke ci gaba tabbatar da tsaro da ba al'umma da dukiyoyinsu kariya a jihar.

Duk wanda ya yi kokarin kawo hargitsi zai gamu da fushin hukuma

DIG Hafiz ya kuma jaddada cewa babban burinsa shine a gudanar da zabe lafiya sannan a kammala lafiya ba tare da yin siyasa da gaba ba.

Ya ce:

"Duk wani dan siyasa da ke son ganin ci gaban Kano, toh zaman lafiya shi zai kawo ci gaban, zaman lafiya shine abun da ake so.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: DSS Ta Kama Yan NNPP 2 Da Ke Shirin Tada Zaune Tsaye Yayin Zaben Gwamna a Kano

"Har ila yau na zo da jawabi, ina mai gargadinsu, wallahi ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk mutumin da ya yi yunkurin ta da zaune tsaye.
"Domin haka, ina mai baku tabbacin cewa duk wanda ya dauki makami ko ya hana wani fita yin zabe, ko ya jikkata wani, Wallahi Tallahi zai gamu da fushin hukuma."

Babu wanda za mu dagawa kafa duk girmansa, yan sanda

Har ila yau, ya kuma sha alwashin cewa babu wanda za a ragawa duk girmansa, don ci gaban Kano da Najeriya, da zaman lafiya shine gaba da komai.

Ya ci gaba da cewa:

"Idan kunne ya ji toh jiki ya tsira, duk wanda kuma yake ganin zai yi abu sabanin wannan toh shege ka fasa."

A halin da ake ciki, hukumomin yan sanda ta tura tare da sake sauya kwamishinonin yan sanda biyar a jihar Kano cikin mako guda, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gaskiya daya ce: Fitaccen Sarki a Arewa ya ba 'yan siyasa shawari game da zaben gwamnoni

Lamarin ya biyo bayan yanayin da jihar ke ciki gabannin zaben gwamna da na yan majalisar jiha da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.

DSS ta kama wasu yan NNPP 2 kan shirin ta da zaune tsaye yayin zaben gwamnan Kano

A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar DSS ta kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da take yi da kokarin kawo hargitsi a jihar Kano yayin zaben gwamna da ke tafe a ranar Asabar, 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel