Malaman Musulunci Sun ba Tinubu, Zababbun Shugabanni Shawara Kafin Shiga Ofis

Malaman Musulunci Sun ba Tinubu, Zababbun Shugabanni Shawara Kafin Shiga Ofis

  • ICICE ta shirya wani zama na musamman domin tattaunawa a kan makomar al’umma bayan siyasa
  • Cibiyar addinin Musuluncin ta gayyaci malamai domin su tattauna a kan zamantakewa bayan zabe
  • Dr. Bashir Aliyu Umar, Dr. Abubakar Sani Birnin Kudu da Janar Usman Kuka Sheka (rtd) suka yi jawabi

Abuja - Legit.ng Hausa ta saurari lacca da aka shirya a masallacin An Nur da ke Wuse II a Abuja a kan rayuwa bayan zabe, ta tsakuro wasu kanun.

Wanda ya jagoranci zaman da aka yi shi ne Dr. Ibrahim Omar Adam Disina, ya kuma rika jefa tambayoyi ga malaman da kuma kakakin sojojin kasa.

A jawabinsa, Dr. Bashir Aliyu Umar ya yi kira ga wadanda suka yi galaba a zabe da su zama masu kankan da kai, su na koyi da Annabi Muhammad SAW.

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Yadda Najeriya Tayi Asarar Naira Tiriliyan 20 a Yunkurin Canza Kudi

Shehin ya bada misali da yadda Manzon Allah ya dukar da kai bayan bude Makkah, sannan ya yi gargadi a kan cin mutuncin malamai a kan siyasa.

Rabon mukaman siyasa

A na sa bangaren, Farfesa Mansur Sokoto ya ce dole shugabanni su rika duba cancanta wajen mukamai, a jawo wadanda suka dace cikin gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Ibn Taymiyyah ya fada a littafinsa na Siyasatus Shar’iyyah, Farfesan ya ce cin amanar Allah SWT ne a rika bada mukami da son zuciya.

Dole shugaba ya san inda aka dosa, idan mutum bai cancanta da kujerar da yake kai ba, a tsige shi,

Tinubu
Tinubu ya lashe zabe Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Twitter

Mansur Sokoto ya ce dole ne idan an shiga ofis a duba alkawuran da aka dauka, sannan a zura idanu a kan abin da Ministoci ko Kwamishinoni suke yi.

Kowa ya yi adalci da gaskiya

Kara karanta wannan

Hangen nesa: Babban malami ya roki Buhari ya kori babban jami'in INEC saboda matsala 1

Kafin nan, Dr. Abubakar Sani Birnin Kudu ya nuna muhimmancin shugabanni su zama masu adalci, ya ce wannan yana cikin koyarwar addinin musulunci.

Malamin akidar ya yi kira ga mutane su sauke nauyin da ke kansu tun daga iyali kuma a fara gyara alaka da Allah SWT, daga nan ne sai komai ya yi kyau.

Malaman musuluncin sun nanata cewa bai kamata talakawa su rika yin fada a kan ‘yan siyasar da ke tsalle daga wannan jam’iyya zuwa wannan jam’iyya ba.

Janar Usman Kukasheka mai ritaya ya yi jawabi a kan inda ya fi kwarewa watau sha’anin tsaro.

Kamar sauran malamai, Janar din ya ce a guji tada tarzoma a zaben jihohi, ya nemi a ba jami’an tsaro hadin-kai, yana mai jaddada kowa yana da rawar takawa.

Kutse miliyan 13 a lokacin zabe

An rahoto Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami yana cewa yunkurin yin kutse a shafukan yanar gizon Najeriya ya kusa dosar miliyan 13 a lokacin zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

Isa Ali Pantami ya ce kafin zabe ana fama da harin kutse 1,550,000 a kowace rana, yayin zaben sabon Shugaban Kasa, adadin kutsen ya karu da miliyan 6.

Asali: Legit.ng

Online view pixel