Zaɓen 2023: Peter Obi Ya Bayyana Takamaiman Abinda Ya Sanya Ya Garzaya Kotu

Zaɓen 2023: Peter Obi Ya Bayyana Takamaiman Abinda Ya Sanya Ya Garzaya Kotu

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya bayyana abinda yake ƙalubalanta a kotu a shari'ar da ya shigar
  • Peter Obi ya bayyana cewa ko kaɗan baya da matsala da nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa
  • Ɗan takarar shugaban ƙasar yace bai yarda da hanyar da aka bi wajen bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen ba

Legas- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, ya bayyana takamaiman abinda yake ƙalubalanta a kotu game da zaɓen.

Peter Obi ya bayyana cewa yana ƙalubalantar hanyar da akabi wajen bayyana Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ba wai sakamakon zaɓen ba.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Tana Ƙasa Tana Dabo Kan Yiwuwar Ƙidayar Bana, Hukumar Tayi Ƙarin Haske

Peter Obi
Zaɓen 2023: Peter Obi Ya Bayyana Takamaiman Abinda Ya Sanya Ya Garzaya Kotu Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Peter Obi ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Arise Tv a ranar Litinin da safe. Rahoton Punch

Jaridar Vanguard ta rahoto ɗan takarar na bayyana cewa ko kaɗan baya da matsala da zaɓaɓɓen shugaban ƙasan domin mutum ne wanda yake matuƙar ganin ƙimar sa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Bani da matsala da Tinubu. Shi mutum wanda nake matuƙar ganin ƙimar sa a matsayin ɗan'uwa sannan nake masa kallon uba."
“Ina kawai ƙalubalantar hanyar da hukumar INEC ta bi wajen bayyana shina matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa. Bani da matsala da bayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa."

Peter Obi yayi kira ga hukumar zaɓe ta ƙasa da ta tashi tsaye wajen ganin ta taimakawa ƴan Najeriya sun ɗaga martabar ƙasar.

"Mun shirya tsaf domin samun sabuwar Najeriya." Dole ne mu yi dukkanin abinda ya dace.

Kara karanta wannan

"Zan Tattauna Da Ƴan Bindiga Idan Aka Zaɓe Ni" Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Kaduna

“Muna buƙatar mu gina hukumomin da zasu ɗaga martabar dimokuraɗiyyar mu ta hanyar koyawa al'umma abinda ayyukan su suke buƙata daga gare su da kuma abinda gwamnati ta ƙunsa."

An Nemi Shugaban APC Na Ƙasa Yayi Murabus Daga Muƙamin Sa

A wani labarin na daban kuma, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, na shan matsin lamba kan sai yayi murabus daga muƙamin sa.

Wannan matsin lambar da yake sha na da nasaba da nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel