Buhari Ya Yi Alkawarin Kakkabe Najeriya Daga Ayyukan Ta’addanci Kafin Ya Sauka

Buhari Ya Yi Alkawarin Kakkabe Najeriya Daga Ayyukan Ta’addanci Kafin Ya Sauka

  • Shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana shirin barin Najeriya ga magajinsa cikin aminci da zaman lafiya
  • Gabanin ranar da zai mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, Buhari ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa, gwamnatinsa za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro
  • Buhari ya ce babban abin da gwamnatinsa ta sa a gaba ba komai bane face tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar ‘yan kasa

Najeriya - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, gwamnatinsa na da shirin yin nasara ga yaki da take da ‘yan ta’adda daban-daban a Najeriya, rahoton jaridar Punch.

Ya kara da cewa, gwamnatinsa ba za ta tsaya ba har sai ta tabbatar da Najeriya ta kubuta daga dukkan nau’in rashinn tsaro kafin ya bar ofis.

Shugaban kasan ya yi magana ne a lokacin da yake kaddamar da wasu ababen hawan jami’an tsaro guda 700 na Ashok Leyland a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Buhari Ya Bada Hakuri Kan Canjin Kudi, Ya Bayyana ‘Yan Takaransa

Buhari ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari kenan | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Buhari ya yabawa sojoji, ya ce suna kokari wajen yaki da ‘yan ta’adda

A bangare guda, shugaban ya yabawa rundunar sojin Najeriya bisa tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma yi alkawarin cewa, kokarinsu ba zai tafi a banza ba, domin sun yiwa kasa hidimar da ake bukata, kamar yadda jaridar Tori ta tattaro.

Ba wannan ne karon farko da shugaban kasa Buhari ke yiwa ‘yan kasa alkawarin kawo karshen rahin tsaro da tashin hankali ba a Najeriya.

Idan baku manta ba, kadan daga manufofin Buhari tun farkon hawa mulkinsa ba komai bane face tabbatar da tsaro, yaki da rashawa, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma tabbatar da samar da abinci ga kasa.

Rashin tsaro: Na sa shugabannin tsaro a gaba kan su karar da 'yan bindigan kasar nan, inji Buhari

Kara karanta wannan

"Shi Ne Daidai" Gwamna Masari Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Bayan Tinubu Ya Ci Zaɓe

A wani labarin na daban, shugaba Buhari ya ce ya tasa shugabannin hafsun tsaron Najeriya a gaba, ya kalubalance su da su tabbatar da kawo karshen ‘yan bindiga a kasar.

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar jaje ga tsohon shugaban PDP na kasa, Adamu Mu’azu bisa rasa dansa da ya yi a barnar ‘yan bindiga.

Buhari ya yi Allah wadai da ayyukan ta’addancin ‘yan bindigan tare da yin alkawarin kawo karshen barnarsu a kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel