Yan Najeriya Basu Shirya Samun Inyamuri a Matsayin Shugaban Ƙasa Ba, Sanatan APC

Yan Najeriya Basu Shirya Samun Inyamuri a Matsayin Shugaban Ƙasa Ba, Sanatan APC

  • Sanatan APC ya bayyana gaskiyar dalilin da ya sanya Inyamurai suka kasa samun mulkin ƙasar nan
  • Uzor Orji Kalu ya bayyana cewa ƴan Najeriya basu shirya samun ɗan ƙabilar Ibo a matsayin shugaban ƙasa
  • Sanatan ya shawarce Inyamurai kan abinda zasu yi idan suna son su samu shugabancin Najeriya

Sanatan APC kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu, ya bayyana cewa ƴan Najeriya basu shirya samun Inyamuri a matsayin shugaban ƙasa ba.

Uzor Orji Kalu ya bayyana hakan ne a yayin wata tattauna da gidan talabijin Channela a shirin su mai suna "The 2023 Verdict" a ranar Laraba. Rahoton Vanguard

Uzor Kalu
Yan Najeriya Basu Shirya Samun Inyamuri a Matsayin Shugaba Ƙasa Ba, Sanatan APC Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A cewar Kalu, zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu ba zai yiwa Inyamurai daɗi ba, domin mutanen yankin suna buƙatar samun goyon baya daga sauran yankunan ƙasar nan kafin wani nasu ya zama shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Babban Dalili Ɗaya Rak Da Ya Sanya Ƴan Najeriya Ba Zasu Zaɓi Tinubu Ba, Datti Baba-Ahmed

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ba wani abin kirkin da Inyamurai za su yi, saboda kafin samun zama shugaban ƙasan Najeriya, akwai buƙatar samun goyon bayan sauran yankunan."

Ɗaya daga cikin ƴan takara 18 da za su fafata a zaɓen shugaban ƙasar a ranar Asabar, Peter Obi, ɗan ƙabilar Inyamurai ne.

Kalu, wanda ɗan takarar Sanatan Abia ta Arewa ne a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, yace Peter Obi ba zai kai labari ba a zaɓen. Rahoton The Cable

"Ina da ƙwarewa sosai, na tsaya takarar shugaban ƙasa a 2007 sannan bana tunanin cewa ƴan Najeriya sun shirya samun shugaban ƙasa ɗan ƙabilar Ibo. Bani da tabbas saboda nayi ƙoƙarin yin hakan.
Akwai goyon bayan sauran yankuna biyar da muke buƙata kuma bana tunanin samu."

Kalu ya kuma bayyana ƙwarin guiwar sa cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, zai yi nasara a jihar Abia da yankin Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Ana Saura Kwana 3 Zaɓe, Atiku Ya Sha Wani Babban Alwashi Kan Tinubu

Zaben Ranar Asabar: Shugaban INEC Ya Gana Da Buhari a Villa

A wani labarin na daban kuma, shugaba Buhari ya sanya labule da shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC).

Ganawar ta su ma zuwa ne a daidai lokacin da ya rage saura kwanaki kaɗan a fara babban zaɓen 2023 a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng