Jerin Manyan Fastocin Najeriya 5 Da Suka Fito Karara Suke Goyon Bayan Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa

Jerin Manyan Fastocin Najeriya 5 Da Suka Fito Karara Suke Goyon Bayan Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa

  • Yan Najeriya da dama na goyon bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben 2023
  • Baya ga tsaffin shugabanni a kasar da suka fito suka mara masa baya don takarar shugaban kasa, matasa da dama suna ganin shine ya dace ya jagoranci kasar
  • Hakazalika, wasu shugabannin addini da suka yi fice a Najeriya sun fito fili sun goyi bayan tsohon gwamnan na Anambra ya zama shugaban kasa

Duk da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da wanda ya fi son ya gaje shi yan Najeriya da dama na goyon bayan Peter Obi don zama shugaban kasa na gaba.

Baya ga fitattun shugabanni da suka bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasar na LP, matasa da dama suna ganin Obi ne ya fi dace wa da aikin.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu: Na Ga Obi Yan Sharban Kuka, Malamin Addini Ya Yi Sabon Hasashe Gabannin Zabe

Peter Obi
Jerin Manyan Sunayen Fastocin Najeriya 5 Da Ke Goyon Bayan Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa Ya Fito. Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

Baya ga su, har wasu fitattun shugabannin addini suma sun nuna goyon bayansu a filli suna cewa ya kamata a gwada tsohon gwamnan na Anambra.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba tare da bata lokaci ba, wannan rubutun zai zayyana manyan fastoci da suka nuna goyon bayansu da Peter Obi a fili, gabanin zabe.

Johnson Suleman
Jerin Manyan Sunayen Fastocin Najeriya 5 Da Ke Goyon Bayan Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa Ya Fito. Hoto: Johnson Suleman
Asali: Facebook

1. Apostle Johnson Suleman

Mamallakin cocin Omega Fire Ministries, OMF, Apostle Johnson Suleman a ranar Lahadi 19 ga watan Fabrairun 2023, ya ayyana goyon bayansa ga Peter Obi.

A wani bidiyo da ya wallafa a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu a shafinsa na Facebook, da Legit.ng ta gani, Suleman ya ce shi da yan gidansa 'suna goyon bayan Obi.'

Chris Oyakhilome
Jerin Manyan Sunayen Fastocin Najeriya 5 Da Ke Goyon Bayan Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa Ya Fito. Hoto: Chris Oyakhilome
Asali: Facebook

2. Chris Oyakhilome

Babban faston cocin Believers Love World da aka fi sani da Christ Embassy, Chris Oyakhilome, a ranar Juma'a, 17 ga watan Fabrairu, ya yi magana cikin hikima.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Ya Hargitse, Jam'iyya Ta Ayyana Gogon Baya ga Peter Obi a Zaben 2023

A bidiyon da ya bazu, faston ya fada wa mambobinsa abin da Ubangiji ya nuna masa game da yan takara uku.

Duk da cewa bai ambaci suna ba amma Chris ya bawa mambobinsa alama cewa dan takarar na uku, 'sunansa na cikin bible'.

Paul Enenche
Jerin Manyan Sunayen Fastocin Najeriya 5 Da Ke Goyon Bayan Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa Ya Fito. Hoto: Paul Enenche

3. Fasto Paul Enenche

Wanda ya kafa cocin Dunamis International Gospel Centre, Fasto Paul Enenche bai yi magana a kaikaice ba wurin goyon bayan Peter Obi.

Yayin wa'azin da ya yi a ranar Laraba, 19 ga watan Fabrairu, Enenche ya yi kira ga yan Najeriya su guji yan takarar da jam'iyyarsu ta jefa Najeriya a cikin halin da ta ke.

A wani bidiyon da Legit.ng ta gani a Twitter a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu, faston yayin sukar tikitin musulmi da musulmi na APC ya ce:

"Mutum daya mai gaskiya da nagarta mai kirki ya rage. Wannan shine babban dan takarar na uku. Ku zabi nagarta, gaskiya da sauki."

Kara karanta wannan

Atiku Ya Kara Shiga Tasku, Gwamnan PDP Ya Yanke Shawara Ta Karshe Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya a 2023

Chibuzor Gift Chinyere
Jerin Manyan Sunayen Fastocin Najeriya 5 Da Ke Goyon Bayan Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa Ya Fito. Hoto: Chibuzor Gift Chinyere
Asali: Facebook

4. Apostle Chibuzor Gift Chinyere

Shugaban cocin Omega Power Ministry (OPM), Apostle Chibuzor Chinyere ya dade yana kira ga yan Najeriya su zabi dan takara da ya dace a babban zaben su zabi Peter Obi.

A Agustan 2022, fastocin ya bayyana Obi a matsayin Musa wanda zai taho ya ceto Najeriya.

Ko a shafinsa na Facebook, ya shawarci yan Najeriya su yi zabe da hikima a zaben da ke tafe.

Odumeje
Jerin Manyan Sunayen Fastocin Najeriya 5 Da Ke Goyon Bayan Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa Ya Fito. Hoto: Prophet Chukwuemeka Ohanaemere
Asali: Facebook

5. Fasto Odumeje

Prophet Chukwuemeka Ohanaemere, wanda ya kafa cocin Mountain of Holy Ghost Intervention Deliverance Ministry a Onitsha, yana daga cikin fastocin da ke goyon bayan Obi.

A wallafar da ya yi, faston ya bayyana goyon bayansa karara ga Obi.

A bidiyon da ya wallafa a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu a shafinsa a Facebook, da Legit.ng ta gani, Odumeje ya shawarci mabiyansa su zabi Obi kuma su dena karbar shinkafa daga wurin yan siyasa.

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

Kalli bidiyon a kasa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel