2023: Karya ta Kare Bayan INEC ta Fitar da Adadin Wakilan Zaben Kowace Jam’iyya

2023: Karya ta Kare Bayan INEC ta Fitar da Adadin Wakilan Zaben Kowace Jam’iyya

  • Jam’iyyun siyasa sun bada sunayen mutane fiye a miliyan 1.5 a matsayin wakilan zabensu a 2023
  • APC, PDP, LP da NNPP su na da wakilai 633, 000 da za su sa masu ido a rumfuna fiye da 176, 846
  • Hukumar INEC ta nuna cewa jam’iyyar PDP mai wakilai 176, 500 ta fi kowa yawan wakilai a zabe

Abuja - A yayin da kwanaki biyar suka rage domin shirya zaben shugaban kasa a Najeriya, hukumar INEC ta fitar da jerin adadin wakilan zaben 2023.

PM News ta rahoto cewa a yammacin Litinin, Hukumar zabe mai zaman kanta, ta wallafa bayanin wakilan zaben da duka jam’iyyun siyasa suka gabatar.

Bayanin da hukumar kasar ta fitar yana dauke da adadin wakilan tattara zabe a duk cibiyoyin da ake da su. Ranar Asabar za a shiga filin zaben sabon shugaba.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Manyan Malaman Addini Da Ke Takara a Zabe Mai Zuwa

Kamar yadda bayanan suka tabbatar, jam’iyyar PDP ce a kan gaba a wajen adadin wakilan zabe, bayan ita kuma sai APC mai-ci, sai jam’iyyun NNPP da LP.

Akwai wakilan zabe 1.57m

Rahoton Vanguard ya tabbatar da cewa jam’iyyu 18 da za su shiga zaben su na da wakilai 1,574,301.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da ta bada sunayen mutane 176,588 ta dauke fiye da 11% na wakilan. Jam’iyyar APC tana biye da ita da adadin wakilai 176,233.

NNPP.
'Dan takaran NNPP a Katsina Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Manyan jam’iyyu hudu da ake gani za a gwabza a zaben shekarar nan watau APC, PDP, LP da NNPP su ke dauke da fiye da 40% na duka wakilan jam’iyyun kasar.

Jam’iyyar NNPP ta bada sunayen mutane 176,200 da za su zama wakilanta a rumfunan zaben da ake da su. Jam’iyyar LP ta zo ta hudu da wakilai 134, 874.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa: Makarantan Legit.ng Sun Tsaida ‘Dan Takara Tsakanin APC, PDP, NNPP da LP

Rahoton ya ce jam’iyyun siyasar sun gabatar da mutane 68, 057 da za su zama wakilai a cibiyar da hukumar INEC za ta tattara kuri’un zaben Jihohi da Abuja.

Kano ta fi kowa wakilan zabe

A yawan wakilan zabe, Jihar Kano ce ta zo farko a Najeriya, a nan APC, PDP da NNPP su na da mutane 145,393. Legas da Ribas suka rufe ukun farko da 178, 441.

Rumfuna 176, 846 ake da su a jihohi 36 da birnin Abuja, amma INEC ta ce zabe zai gudana ne a rumfuna 176, 606 saboda rashin masu zabe a wasu wuraren.

APC za ta zarce a mulki Inji Kalu

An samu labari, a ra’ayin Sanata Orji Uzor Kalu, ‘Dan takaran APC yana kan hanyar zama Shugaban Najeriya domin ‘Yan Arewa na kaunar Asiwaju Bola Tinubu.

Tsohon Gwamnan ya ce Tinubu yana tare da Yarbawa, kuma Ibo za su zabe shi sannan ya ce a Gwamnonin PDP, akwai wadanda APC suke yi wa aiki a 2023.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe: PDP Ta Hadu Da Gagarumin Cikas a Kano, Tsagin Shehu Sagagi Sun Yi Maja Da Jam’iyyar Kwankwaso

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng