Asiwaju Ya Kara Karfi a Arewa: Dan Takarar Gwamnan LP a Kano Ya Yi Maja Cikin APC

Asiwaju Ya Kara Karfi a Arewa: Dan Takarar Gwamnan LP a Kano Ya Yi Maja Cikin APC

  • Yan kwanaki kafin babban zabe, jam'iyyar Labour Party ta hadu da gagarumin cikas a jihar Kano
  • Dan takarar gwamnan LP a jihar ta arewa ya rushe tsarinsa sannan ya yi maja da jam'iyyar APC mai mulki
  • Bashir Ishaq Bashir, ya kuma ayyana goyon bayansa ga takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC

Kano - Dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour Party (LP) a jihar Kano, Bashir Ishaq Bashir, ya yi murabus daga jam'iyyar a hukumance.

Ya ayyana biyayyarsa da goyon bayansa ga jam'iyyar All Progressives Congress (APC). mai mulki, rahoton The Nation.

A karshen makon, Bashir, ya janye goyon bayansa ga Peter Obi wanda ke takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP sannan ya ayyana goyon bayansa ga Asiwaju Bopla Ahmed Tinubu na APC.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Tinubu Zai Shayar Da Atiku Mamaki a Arewa Maso Gabas - APC

Obi da Tinubu
Asiwaju Ya Kara Karfi a Arewa: Dan Takarar Gwamnan LP a Kano Ya Yi Maja Cikin APC Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Takenmu shine Sabon Lale ga Asiwaju/Shettima, Bashir

Ya kuma yi bayanin dalilin da yasa sauran jiga-jigan jam'iyyar suka kauracewa gangamin yakin neman zaben jam'iyyar a Kano, wanda aka yi a yankin Sabon Gari a ranar 22 ga watan Janairu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Za mu koma inuwar jam'iyyar All Progressives Congress, kuma ina fatan sanar da ku cewa yanzun nan muka kammala taron kwamitinmu inda muka tattauana bayanan da muka samu daga mazabunmu.
"Cewa bayan an zartar da hukunce-hukunce: Cewa a matsayin gamayyar dan takarar gwamnan Labour Party, sanatoci da majalisar wakilai, yan takarar masalisar jiha, shugaba da mambobin kwamitin yakin neman zabe, mambobin kwamitin yakin neman zaben gwamna da jagprorin sashi da jiha mun yanke shawarar lamuncewa takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
"Mun kuma yanke shawarar hade tsarin siyasarmu da ke nan don aiki wajen tattara masu zabe don tabbatar da nasarar Tinbubu a matsayin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

PDP Yaudara Ce: Mataimakin Shugaban Jam'iyyar Ya Ce Ya Yi Murabus

"Sunan da za a sanmu da shi shine Game Changers for Asiwaju/Shettima 2023. takenmu shine “Sabon Lale”…Za mu koma inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Party.”

Gwamnonin G-5 sun rabu gida uku gabannin babban zaben 2023

A wani labarin kuma, gwamnonin PDP wadanda ake kira da G-5 sun samu rabuwar kai a tsakaninsu kan dan takarar da za su marawa baya a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Gwamnoni biyu na goyon bayan Bola Tinubu na APC, mutum daya na tare da Peter Obi na Labour Party yayin da sauran biyun ke tare da Atiku Abubakar na PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel