Dan Takarar Gwamnan Da Shugabannin LP Sun Kauracewa Kamfen Din Peter Obi a Kano

Dan Takarar Gwamnan Da Shugabannin LP Sun Kauracewa Kamfen Din Peter Obi a Kano

  • Baraka ta kunno kai a jam'iyyar Labour Party (LP) reshen jihar Kano ana saura yan kwanaki a shiga watan zabe
  • Dan takarar gwamnan LP a Kano da shugabanni da jiga-jigan jam'iyyar a jihar sun kauracewa gangamin kamfen din Peter Obi
  • Majiya ta ce sun ki halartan kamfen din ne saboda ba sanar da su ba har sai ana gobe za a yi

Kano - Dan takarar gwamnan Labour Party (LP) a jihar Kano, Bashir I. Bashir da sauran shugabannin jam'iyyar sun kauracewa gangamin kamfen din Peter Obi a jihar.

Bashir bai halarci gangamin yakin neman zaben jam'iyyar da aka gudanar a filin wasa na Kano Pillars da ke yankin sabon gari ba a ranar Lahadi, 22 ga watan Janairu, rahoton Daily Trust.

Kamfen din Obi a Kano
Dan Takarar Gwamnan Da Shugabannin LP Sun Kauracewa Kamfen Din Peter Obi a Kano Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Hakazaika, ko sama ko kasa ba a ga shugabannin jam'iyyar da shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na LP, Mohammed Zarewa; jagoran kamfen din Peter Obi a jihar, Balarabe Wakili da Idris Dambazau ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Bullo a Kudu, Sun Gindaya Sharadi Kafin Su Bari ayi Zabe

Da aka tuntube shi, Bashir ya ce shugabannin jam'iyyar za su hadu sannan su sake bitar lamarin da ya kai ga kamfen din sannan su yi jawabi ga manema labarai cikin awanni 48 masu zuwa amma ya ki yin karin bayani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiya ta fadi dalilin rashin ganin shugabannin LP a gangamin Obi a Kano

Sai dai kuma, wani majiya da ya nemi sakaya sunansa, ya bayyana cewa matsalar da shugabannin ke da shi da dan takarar mataimakin shugaban kasa, Datti Baba-Ahmed ne ba da Obi ba, rahoton Daily Nigerian.

Ya ce shugabannin jam'iyyar a jihar sun yi mamaki da rashin jin dadi cewa ba a tafi da su harkokin kamfen din ba kuma cewa ba a tuntubi kowannensu ba har sai a yammacin ranar Lahadi lokacin da Obi ke hanyar zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Manyan Jihohi 2 da APC Ke Shirin Kwacewa Daga Hannun PDP da Dalili

"Obi ya sanar da su da farko cewa Baba-Ahmed ne zai jagoranci tattara mutane a yankin arewa da taimakonsu sannan shi Obi ya saki kudin kamfen amma mataimakin shugaban kasa ya ki shigar da su harkoki saboda wani dalili da shi kadai ya sansa.
"Ta yaya za ka zo kamfen a Kano sannan ba za ka tafi da dan takarar gwamna da sauran shugabanni ba?" ya tambaya.

Zan hada kan Najeriya idan na zama shugaban kasa, Obi a Kano

A halin da ake ciki, Obi ya sanar da dandazon magoya bayansa a wajen yakin neman zabe cewa idan aka zabe shi zai ci gaba da hada kan yan Najeriya da kuma dakile abubuwan da za su ci gaba da raba kan kasar.

Ya bayyana cewa gwamnatocin baya da sauran yan siyasa sun yi amfani da kabilanci da addini wajen mayar da kasar baya.

A wani labari na daban, mambobin jam'iyyar NNPP a jihar Kano sun sauya sheka zuwa APC gabannin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel