Za Mu Ba Atiku Mamaki a Arewa Maso Yamma – In ji Jam’iyyar APC

Za Mu Ba Atiku Mamaki a Arewa Maso Yamma – In ji Jam’iyyar APC

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta ce dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu shine zai lashe zaben 2023
  • APC ta yi hasashen cewa Tinubu zai yi kasa-kasa da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar a yankinsa na arewa maso gabas
  • Ta ce duk da makarkashiyan da ake mata a kan manufar sauya kudi, mutanen Borno Tinubu za su yi a zaben shugaban kasar gobe

Borno - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce za ta lallasa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a yankinsa na arewa maso gabas.

A wata sanarwa da ya saki, mataimakin sakataren labarai na jam'iyyar APC na kasa, Hon. Murtala Yakubu Ajaka, ya ce manufar kudi ba zai hana mutanen arewa maso gabas zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ba.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Zai Girgiza da Sakamakon Zabe a Arewa Maso Yamma, Jigo Ya Fasa Kwai

Atiku Abubakar and Bola Tinubu
Za Mu Ba Atiku Mamaki a Arewa Mmaso Yamma – In ji Jam’iyyar APC Hoto: Atiku Abubakar/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewarsa, gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na APC da aka yi a Borno a ranar Asabar, 18 ga watan Fabrairu ya tabbatar da hakan, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Mutanen Borno APC suke yi a 2023, Inji jigon APC

Ajaka wanda ya halarci gangamin kamfen din ya yi godiya ga gwamnan jihar da mutanen Borno da suka yi tururwar fitowa don marawa dansu kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashin Shettima baya, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta ce:

"Fitowar na Borno sako ne karara ga PDP da dan takararta na shugaban kasa cewaa abun mamaki na jiransu a yankin arewa maso gabas.
"Mutanen jihar Borno sun yi magana da kakkausar murya kuma sakon a bayyane yake karara cewa su na APC ne."

Ajaka ya nuna karfin gwiwar cewa APC ba wai lashe zabe kawai za ta yi a arewa maso gabas ba amma za ta yi nasara ne a babban zaben a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Toh fa: Atiku da Tinubu sun tsufa, dattawan Arewa sun fadi mafita a zaben 2023

Gwamnonin PDP sun dauki bangare cikin yan takarar shugaban kasa

A wani labarin, gwamnonin PDP biyar da ake yi wa lakani da G-5 sun bayyana matsayinsu kan yan takarar shugaban kasar da za su marawa baya a babban zaben 2023 mai zuwa.

Hasashe sun nuna cewa Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde suna tare da Asiwaju Bola Tinubu yayin da Samuel Ortom ya fito ya nuna cewa Obi yake yi.

Sauran mutane biyu da suka rage Gwamna Okezie Ikpeazu na Abia da Ifeanyi Unguanyi na Enugu sun yarda za su marawa dan takararsu na PDP, Atiku Abubakar baya a zaben shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel