PDP Yaudara Ce: Mataimakin Shugaban Jam'iyyar Ya Ce Ya Yi Murabus

PDP Yaudara Ce: Mataimakin Shugaban Jam'iyyar Ya Ce Ya Yi Murabus

  • David Chigbu, mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na jihar Abia ya fita daga jam'iyyar ya goyi bayan Sanata Abaribe na jam'iyyar APGA
  • Chigbu ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ta PDP ne a ranar Alhamis yana mai cewa ita ta jefa jihar cikin mummunan halin da ta ke ciki yanzu
  • Tsohon mataimakin ciyaman din na PDP a Abia ya kira tsohuwar jam'iyyarsa tarin makaryata kuma masu yaudara don haka ya bar su kafin jam'iyyar ta gama rushewa

Jihar Abia - Mataimakin shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Abia, David Chigbu, ya yi murabus daga jam'iyyar, rahoton The Punch.

Ya kuma bayyana goyon bayansa ga Sanata Eyinnaya Abaribe, wanda ke takarar kujerar sanata na Abia South karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, da ke fafatawa da Gwamna Okezie Ikpeazu.

Kara karanta wannan

Jemage: Bani Maka Kamfen, Ba Kuma Na Hamayya Da Kai, Wike Ga Bola Tinubu

Jam'iyyar PDP
PDP Yaudara Ce: Mataimakin Shugaban Jam'iyyar Ya Ce Ya Yi Murabus. Hoto: The Punch

Abaribe ya fice daga PDP ana daf da zaben fidda gwani na jam'iyyar a bara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chigbu, cikin sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce tsohuwar jam'iyyarsa 'yaudara ce' kuma ita ta jefa jihar cikin matsaloli.

Ya kuma bayyana jam'iyyar a jihar da gwamnatin jihar a matsayin taron makaryata, wadanda suke daf da shan kaye.

Ya kara da cewa:

"Dole ya sa na fita daga jam'iyyar kafin rushewar abin da ya yi saura a PDP."

Abaribe, ya ce, alama ne na gaskiya da rikon amana, ko da lokacin da ake masa bita da kulli.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Abia karkashin PDP ta zama abin dariya da raha tsakanin yan Najeriya musamman a yanzu.
"Ya zama dole mu hada hannu mu ceto jihar daga hannun wadanda suka rike jihar kamar tasu su kadai har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Wasu Manyan Jiga-Jigan Jam'iyyar APC Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP a Jihar Bauchi

"Murabus na aiki ne na kishin kasa don na hada kai da sauran yan Abia da ke da kyakkyawar niyya don dakatar da PDP daga ci gaba da yi wa jiharmu fyade tare da kokarin da suke yi na kwashe dukiya. Abin ya isa haka.
"Na yi murabus ne domin PDP yaudara ne. Ina kallon PDP a matsayin jam'iyyar da ke rudar yan Abia. PDP na da dan takarar shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da kuma tsohon dan takarar gwamna Farfesa Uche Ikonne wanda ya rasu yanzu akwai sabon dan takar Cif Okey Ahaiwe."

Dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour ya koma PDP a Osun

A wani rahoton kun ji cewa dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour a zaben gwamnan Osun na 2022, Lasun Yusuf ya koma jam'iyyar PDP.

A rahoton da Leadership ta wallafa, gwamnan jihar Osun Sanata Ademola Adeleke ne ya sanar da hakan yayin taron yakin neman zaben shugaban kasa na PDP da aka yi a jihar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC A Kwara Ta Dakatar Da Sakatarenta, Ta Bayyana Dalili

Asali: Legit.ng

Online view pixel