Wannan Lokacinku Ne Ku Samar da Shugaban Kasa, Atiku Ga Mutanen Adamawa

Wannan Lokacinku Ne Ku Samar da Shugaban Kasa, Atiku Ga Mutanen Adamawa

  • Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar, ya kammala yakin neman zabensa a Adamawa yau Asabar
  • A ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 watau nan da mako ɗaya INEC ta tsara gudanar da zaɓen shugaban kasa
  • Atiku ya yi jawabi mai jan hankali ga mutanen Adamawa game da mutanen da zasu damƙa wa amanarsu

Adamawa - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya roki mazauna Adamawa su kalli zaɓe mai zuwa a matsayin lokaci mai tsada da zasu zaɓe shi shugaban kasa.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya faɗi haka ne a wurin ralin kamfen PDP na karshe da ya gudana a jihar ranar Asabar, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Atiku Abubakar.
Wannan Lokacinku Ne Ku Samar da Shugaban Kasa, Atiku Ga Mutanen Adamawa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Wazirin Adamawa ya ce ya shirya muhimman kudirori 5 a cikin kunshin kundin manufofinsa kuma zai tabbatar da ya cika dukkan alƙawurran da ya ɗauka.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamna Wike Ya Bayyana Wanda Yake Goyon Baya Saura Kwana 7 Zaben 2023

Premium Times ta rahoti a kalamansa yana cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Na ɗaukar maku alkawari ba zan baku kunya ba, idan kuka bamu amana zamu tabbata alƙawurran da muka ɗauka ba su tafi a iska ba ta yadda Najeriya zata dunƙule da zaman lafiya."
"Zamu gina tsayayyen tattalin arziki ga ƙasarmu, nagartaccen ilimi ga 'ya'yanmu, mu baiwa gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi cikakken iko da iya arzikin da Allah ya bamu."
"Waɗan nan ne manyan kudirorin da PDP ta yi alƙawari samarwa. Saboda haka ina jaddada maku aniya ta na fabbatarr da waɗannan abu guda biyar."

Lokaci ya yi da zaku bani amanarku - Atiku

"A jihar Adamawa, wannan ce damarku ta zaɓen PDP ta hau karagar mulki, idan kuka zaɓi PDP ta ci gaba da mulki a jihar nan, ba sai na faɗa maku aikin zan yi wa Adamawa, arewa maso gabas da Najeriya baki ɗaya ba."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Wike Ya Yi Magana Ta Karshe Kan Yuwuwar Sulhu da Atiku Ana Dab da Zaɓen 2023

"Kunsan cewa ni mutum ne mai magana ɗaya saboda haka ina kira gareku ku dangwalawa APC tun daga sama har ƙasa. Karku bari wani ya sauya maku tunani da Farfaganda."

- Atiku Abubakar.

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Bayyana Wanda Yake Goyon Baya Saura Kwana 7 Zaben 2023

Gwamna Wike ya ƙara hannun ka mai sanda, ya nuna goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC, Bola Tinubu.

Da yake jawabi a wurin ralin PDP na ƙarshe a jihar Ribas, gwamna Wike ya ce yana goyon bayan matsayar da gwamnonin APC suka amince da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel