Zaben 2023: Shin Tinubu Yana Da Lafiyar Da Zai Iya Shugabancin Najeriya, El-Rufai Ya Bada Amsa

Zaben 2023: Shin Tinubu Yana Da Lafiyar Da Zai Iya Shugabancin Najeriya, El-Rufai Ya Bada Amsa

  • Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce yana da dalilin da yasa baya alkalanci kan lafiyar mutane
  • A cewar gwamnan, yin hakan kamar yiwa kai ba'a ne saboda ba wanda yasan gawar fari, musamman ga wanda ya haura shekara 60
  • Sai dai gwamnan ya ce a tsahon lokacin da ya shafe da Tinubu ya tabbatar yana da lafiyar kwakwalwar da zai iya shugabantar Najeriya

Kaduna - Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna, ya bayyana halin da lafiyar Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugabancin kasa a inuwar jam'iyyar APC ke ciki.

Gwamnan ya ce shi bashi da masaniya akan rahoton lafiyar Tinubu, amma ya san duk wanda ya haura shekara 60 yana fama da matsalolin rashin lafiya, kamar hawan jini.

Bola Tinubu
Ko Lafiyar Tinubu Ta Isa Ya Shugabanci Najeriya? El-Rufai Ya Magantu. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

El-Rufai ya bayyana babban abun da ke damun Tinubu na rashin lafiya

Kara karanta wannan

El-Rufai: Yadda Yan Takarar Shugaban Ƙasa 2 Suka Samu Ɗaruruwan Sabbin Miliyoyin Takardun Naira

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin tattaunawar sa da Premium Times.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Cikin ba'a, gwamnan ya ce:

"Ba ni da hawan jini; ni ke ba wa wasu hawan jini."

Camfi ne yanke hukunci akan lafiyar wani, in ji El-Rufai

Ya kara da cewa baya son yanke hukunci a lafiyar mutane saboda zai zama abin kunya a wajen sa saboda shi ya ga darasi.

Gwamnan ya bada labarin cewa:

''Har yanzu ina tuna kwamitin binne Dr. Nnamdi Azikiwe lokacin da aka yada jita-jita ya mutu, Okafor da Mbadiwe suka cusa kan su a kwamitin. Sai aka gano Azikiwe bai mutu ba, kuma, gaba daya suka riga shi mutuwa.''

El-Rufai ya sake bayyana wani dalilin da ya sa baya hukunci akan lafiyar mutum, musamman wanda suka haura 60, ba wanda ya san wanda zai fara mutuwa.

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Yarda da Ganduje, Ya Jadadda Kutun-Kutun din da Buhari Yake Shiryawa

Ya bayyana cewa yana tunanin kamar Tinubu ya na da matsala a kafarsa, ya yi ikirarin cewa Tinubu yana cikakkaiyar lafiyar kwakwalwa da zai iya jagorantar kasar nan a iya lokacin da suka shafe suna tattaunawa.

Abin da yasa na ce Tinubu ya fi ni lafiya, Sanata Kashim Shettima

A gefe guda, Sanata Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya bayyana cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fi shi lafiya.

Shettiman ya bayyana hakan ne cikin wata hira da aka yi da shi a dandalin sada zumunta na Facebook yayin bayyana manufofin siyarsa da ta Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel