El-Rufai Ya Yarda da Ganduje, Ya Jadadda Kutun-Kutun din da Buhari Yake Shiryawa

El-Rufai Ya Yarda da Ganduje, Ya Jadadda Kutun-Kutun din da Buhari Yake Shiryawa

  • A daren yau Nasir El-Rufai ya yi wa al’umma jawabi na musamman kan maganar yin canjin kudi
  • Gwamnan jihar Kaduna ya cigaba da yin tir da matakin da gwamnatin tarayya da CBN suka dauka
  • El-Rufai ya ce ana so a gagara yin zaben 2023 ta yadda za a kafa gwamnatin rikon kwarya a Najeriya

Kaduna - A wani jawabi da ya yi a daren Juma’a, Nasir El-Rufai ya soki tsarin canza kudi da gwamnan babban bankin CBN ya kawo a kasar nan.

Gwamnan jihar Kaduna ya shaidawa al’ummarsa da gan-gan aka yi sanadiyyar karancin takardun kudi saboda a nemi hanyar hana yin zabe.

Malam Nasir El-Rufai yake cewa idan aka gamu da matsala wajen shirya zabuka, a karshe za a kafa gwamnatin rikon kwarya ne ta jagoranci kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Bayyana Yadda Buhari da CBN Suka Jawowa Jam’iyyarsu Bakin Jini

Mai girma Gwamnan ya yi mutanen Kaduna jawabi na musamman, Punch ta ce El-Rufai yana zargin ana so Bola Tinubu ya ji kunya a zaben 2023.

Bangaren jawabin Nasir El-Rufai

“Ya kamata mutanen jihar Kaduna da na Najeriya su fahimci cewa duk da kyawawan niyyoyin wannan tsari da ake nunawa, akasin haka ya jawo aka fito da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda suka sha kashi zaben samun takaran Gwamna da na shugaban kasa a zaben fita da gwanin jam’iyyar APC a Yunin 2022 suka kawowa shugaban kasa tsarin.
Asiwaju Bola Tinubu yana zama ‘dan takara a Yunin 2022, kuma aka ga bai dauki daya daga cikinsu a matsayin abokin takara ba, sai aka kirkiro tsarin canza kudi.

- Nasir El-Rufai

El-Rufai
Gwamna Nasir El-Rufai Hoto @GovKaduna
Asali: Twitter

The Nation ta rahoto Gwamnan mai barin gadon-mulki a Mayu mai zuwa yana cewa an cin ma manufar jawowa jam’iyyar APC bakin jini wajen masu zabe.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Gwamnati Tana Rokon a Sasanta, Amma Mun Ki Yarda Inji El-Rufai

Gwamnatin rikon kwarya

A cewar Malam El-Rufai, idan aka zarce da wahalar fetur da aka kirkiro tun Satumban 2022 game da canjin kudi, ba za a iya yin zaben shugabanni ba.

Ko da kuwa ba ayi zabe ba, dole wadanda ke kan mulki za su bar ofis, tsohon Ministan birnin tarayyan ya ce a nan za a kafa gwamnatin rikon kwarya.

An rahoto El-Rufai yana cewa gwamnatin riko za ta kasance a karkashin jagorancin wani tsohon Janar a gidan soja, Gwamnan bai yi wani karin bayani ba.

Zargin da Ganduje yake yi

An ji labari cewa Gwamnan Kano ya zargi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ‘kashe’ Jam’iyyar APC a lokacin da zai bar mulki a watan Mayun 2023.

Abdullahi Ganduje ya ce gwamnatin Buhari tana kokarin kafa gwamnatin rikon kwarya irinta Cif Ernest Shonekan a 1993 a maimakon a shirya zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel