Dalilin da Yasa Nace Tinubu Ya Fi Ni Lafiya, Inji Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa a APC, Kashim Shettima

Dalilin da Yasa Nace Tinubu Ya Fi Ni Lafiya, Inji Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa a APC, Kashim Shettima

  • Kashim Shettima ya bayyana kadan daga lafiyar Tinubu, inda yace ya ma fi shi isasshen lafiya idan aka yi duba ga wasu dalilai
  • Shettima ya bayyana hakan ne tare da yin tsokaci ga wasu shugabannin waje da suka yi mulki lokacin da suke jinya
  • ‘Yan Najeriya suna ci gaba da nuna damuwa kan lafiyar Tinubu, ana ganin ba zai iya ji da matsalolin da kasar ke ciki ba a yanzu

Najeriya - Mai takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC, Kashim Shettima ya bayyana cewa, dan takarar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya fi shi cikakken lafiya.

Shettima ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi dashi a kafar Facebook, inda ya bayyana manufofi tare da yin fashin baki game da matsayar siyasarsa da Tinubu har da APC.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo da Komai Baya, Ya Fadi Gaskiyar Batun Haduwarsa da Gwamnonin PDP

Wannan tattaunawa an yi ta ne a shirin Fashin Baki da Bula Bukarki, Abban Hikima da Jaafar Jaafar tare da Shettima a matsayin babban bako a daren jiya Lahadi 1 ga watan Disamba.

Tinubu ya fi ni koshin lafiya
Dalilin da Yasa Nace Tinubu Ya Fi Ni Lafiya, Inji Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa a APC, Kashim Shettima | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Idan baku manta ba, ‘yan Najeriya da dama na ci gaba da nuna damuwa da dasa alamomin tambaya game da lafiyar Tinubu tun farkon tsayawarsa takara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lafiyar Tinubu lau, inji Shettima

Da yake bayyana halin da dan takarar ke ciki, Shettima ya ce Bola Tinubu lafiyarsa kalau, kuma ba shi da wata cuta da ke damunsa a yanzu.

A cewar Shettima, an sha samun shugabannin duniya da ke mulki a kan keken kuragu, amma sun yi tasiri wajen habaka tattalin arzikin kasashensu.

A gefe guda, ya ce aikin shugaban kasa ba kamar leburanci ne da ake shan wahalar daukar kaya ba, don haka yana da yakinin tabbas zai iya yin mai yiwuwa wajen kawo ci gaba Najeriya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Tinubu ya fasa kwai kan ganawa da gwamnonin G-5, ya ce akwai lauje cikin nadi

Da yake amsa tambayar Bula Bukarti kan meye bayani kan lafiyar Tinubu, Shettima ya ce:

“Wallahi ba maganar siyasa zan yi maka ba, Bola Ahmad Tinubu yana cikakken koshin lafiya. Ka ga mulkin nan, ba aikin leburancin daukar siminta bane fa.”

Tinubu ya fi ni koshin lafiya, cewar Shettima

Hakazalika, an dago tambaya game da yanayin da Tinubu ke nunawa a wajen tarukan kamfen, inda aka ce yana yawan kuskurewa da fadin maganganu masu dauka hankali.

Hakazalika, ya ce Tinubu ya fi cikakken lafiya, amma mutane basu san da hakan ba.

Da yake bayyana dalilinsa, Shettima ya ce:

“Kowa ma zai iya yi kuskure, kuma bugu da kari, ya fi ni koshin lafiya.
“Na daya, mun yi tafiya dashi, bashi da ciwon suga, ni ina da ciwon suga. Ba shi da hawan jini. Maganar karkawa kuwa, da zarar ya samu isasshen bacci duk yana tafiya.”

Tinubu dai na yawan subut da baka da kuma kawo maganganu masu ban mamaki da ke dasa alamar tambaya ga lafiyarsa.

Kara karanta wannan

PDP: Sabon Bayani Ya Fito Yayin Da Gwamna Ortom Ya Magantu Kan Yarjejeniyar Da Aka Ce G5 Ta Yi Da Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel